Zambar N6.3bn: EFCC Ta Kammala Gabatar Da Shaidu A Shari'ar Jonah Jang, hukunci ya rage

Zambar N6.3bn: EFCC Ta Kammala Gabatar Da Shaidu A Shari'ar Jonah Jang, hukunci ya rage

  • Kotu na gab da yanke hukunci kan shari'ar da EFCC ke yi kan tsohon gwamnan jihar Plateau
  • EFCC na zargin tsohon gwamnan da almundahanan sama da bilyan shida na kudin jiharsa lokacin da yake mulki
  • Hukumar yaki da rashawa ta ce ta gabatar da shaidu 14 da ke nuna gaskiyar zargin da suka masa

Jos - Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta kammala gabatar da shaidu a shari'ar da take wa tsohon gwamnan jihar Plateau, Jonah David Jang.

Hukumar ta gurfanar da Jonah Jang tare da wani tsohon ma’aikacin kudi a ofishin sakataren gwamnatin jihar, Yusuf Pam a gaban mai shari’a C. L. Dabup na babbar kotun jihar Plateau, a Jos.

Ana zarginsu da sama da fadi da kudin al'ummar jihar Plateau N6.2bn.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC a Kano: An nemi a soke shirin yayin da aka kaddamar da bincike kan kisan mutane 3

Jonah Jang
Zambar N6.3bn: EFCC Ta Kammala Gabatar Da Shaidu A Shari'ar Jonah Jang, hukunci ya rage Hoto: EFCC
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar a jawabin da ta fitar ranar Alhamis, tace:

"EFCC ta kammala gabatar da shaidun ne bayan ta kira shaidu goma sha hudu tareda gabatar da wasu hujjoji inda take tuhumar tsohon gwamnan da Pam da laifin hadin baki, cin amana da karkatar da dukiyar jihar na kudin da ya kai kimanin naira biliyan shida da miliyan dari uku.
A zaman kotun na karshe, EFCC ta gabatar da mai bayar da shaida na goma sha hudu, wato wani jami’in hukumar ICPC, Mai suna Taiwo Oloronyomi wanda ya bayar da shaida akan su
Sai dai kuma lauyan wanda ake tuhuma na biyu ya ki amincewa da wasu takardun shaidu da aka gabatar a gaban kotun."

Asali: Legit.ng

Online view pixel