Hotunan shugaba Buhari yayinda ya dira birnin Madrid, Kasar Andalus

Hotunan shugaba Buhari yayinda ya dira birnin Madrid, Kasar Andalus

  • Yan kwanaki bayan dawowa daga Malabo, Shugaba Buhari ya yi tafiya kasar Andalus ranar Talata
  • Shugaban kasan ya samu rakiyar Ministocinsa bakwai da shugabannin wasu hukumomi uku
  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kwanaki uku kacal zai yi ya dawo gida

Madrid - Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Madris, kasar Spain da daren Talata, 31 ga watan Mayu, 2022.

Shugaban kasa ya samu kyakkyawan tarba dgaa wajen jami'in Gwamnatin kasar Andalus.

Hadimin shugaban kasa kan gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ya saki hotunan.

Shugaba Buhari
Hotunan shugaba Buhari yayinda ya dira birnin Madrid, Kasar Andalus Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sugaba Buhari
Hotunan shugaba Buhari yayinda ya dira birnin Madrid, Kasar Andalus Hoto: BUhari Sallau
Asali: Facebook

Shugaba Buhari
Hotunan shugaba Buhari yayinda ya dira birnin Madrid, Kasar Andalus Hoto: BUhari Sallau
Asali: Facebook

Hotunan shugaba Buhari yayinda ya dira birnin Madrid, Kasar Andalus
Hotunan shugaba Buhari yayinda ya dira birnin Madrid, Kasar Andalus Hoto: BUhari Sallau
Asali: Facebook

Tafiyar Buhari Andalus

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, a ranar Talata yace shugaban Spain ne ya gayyaci mai Shugaba Buhari .

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai shilla Madrid, kasar Spain yau Talata

Ya bayyana cewa Buhari za tafi tattauna abubuwa da dama masu muhimmanci kuma zasu rattafa hannu kan wasu yarjejeniya da suka kulla a baya.

A cewarsa, abubuwan da za'a tattauna kai sun hada da hadin kai wajen kawar da matsalar rashin tsaro, harkokin al'adu, yarjejeniyar mikawa juna mai laifi, dss.

Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Antoni Janar, Abubakar Malami (SAN); Ministan masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Adeniyi Adebayo; Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed da Ministan harkokin cikin gida, Rauf AregbeSola.

Sauran sun hada da Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare; mataimakin Ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora; NSA Babagana Munguno; Shugaban hukumar leken asiri, Amb Ahmed Rufa'i Abubakar da shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng