Da duminsa: Wani abu mai fashewa ya sake tashi a wata jihar arewacin Najeriya

Da duminsa: Wani abu mai fashewa ya sake tashi a wata jihar arewacin Najeriya

  • Wani abu mai fashewa ya sake tashi a garin Kabba da ke karamar hukumar Kabba-Bunu, jihar Kogi
  • An gano cewa, lamarin ya faru ne wurin karfe 9:15 na daren Lahadi a wani gidan giya da ke garin Kabba
  • 'Yan sanda sun tabbatar da cewa jami'ansu na kan lamarin duk da ba a rasa ko rai daya ba a yayin da lamarin ya faru

Kabba, Kogi - Rundunar 'yan sandan jihar Kogi a ranar Lahadi ta tabbatar da fashewar wani abu a garin Kabba da ke karamar hukumar Kabba-Bunu ta jihar.

Kakakin rundunar, William Ovye-Ayaz, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Lokoja, ya ce babu wanda ya rasa ransa.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce fashewar abun ya faru ne a wata mashaya ta Omofemi da ke Kwatas din Okepadi, Kabba, wurin karfe 9:15 na daren Lahadi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Da duminsa: Wani abu mai fashewa ya sake tashi a wata jihar arewacin Najeriya
Da duminsa: Wani abu mai fashewa ya sake tashi a wata jihar arewacin Najeriya. Hoto daga premiumtimeng.com
Asali: UGC
"A halin yanzu, babu wanda ya rasa ransa amma kujeru da tebura da ginin duk sun ragargaje ta yadda har yanzu ba a san tushen fashewar abun ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Tuni kwamishinan 'yan sanda, Edward Egbuka, ya umarci rundunar cire bom da masu bincike da su karasa wurin don tantance yanayin fashewar abun.
"'Yan sandan suna kan lamarin a halin yanzu, jami'an mu sun mamaye wurin har sai an kammala bincike.
"Abun takaici ne yadda 'yan ta'adda suka fito domin hargitsa zaman lafiyan da muke mora a Kogi.
"Ba za mu yi kasa a guiwa ba har sai mun bankado wadannan 'yan ta'addan kuma su gane amfanin kiyaye zaman lafiya a al'umma," ya ja kunne.

SP Ovye-Ayaz ya yi kira ga jama'ar Okepadi da Kabba da su kwantar da hankulansu, su cigaba da lamurransu ba tare da tsoro ba saboda 'yan sanda na kan lamarin, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kala-Balge: Zulum ya kai ziyarar jaje ga iyalan mutane 30 da aka yanka a Borno

NAN ta ruwaito cewa, fashewar abun da ya janyo cece-kuce kan cewa bam ne ko tukunyar gas, ya faru a ranar 11 ga watan Mayun a gidan giya da ke Lewu Junction a garin Kabba.

An rasa rayuka daga cikin mutane 16 da lamarin ya shafa.

Wani abin fashewa ya tashi da daliban makaranta a jihar Kano

A wani labari na daban, labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa wani abin fashewa ya tashi a jihar Kano, Arewa maso yammacin Najeriya.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa ya tashi a Aba Road da ke Unguwar Sabon Gari a birnin Kanon.

Shugaban Kasuwar Sabon Gari Nafi'u Nuhu Indabo ya tabbatar da cewa lamarin ya rutsa da mutane da dama ciki har da yara ƴan makaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng