Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon gwamna kan zargin hannu a damfarar N80b ta dakataccen AGF

Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon gwamna kan zargin hannu a damfarar N80b ta dakataccen AGF

  • Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari kan alaka da N80 biliyan da dakataccen AGF Ahmed Idris ya kwashe
  • A yayin bincike, hukumar EFCC ta gano wata harkallar kudade har N20 biliyan tsakanin tsohon gwamnan da Ahmed Idris
  • Yari ba sabon shiga bane wurin shiga komar EFCC, ko a shekarar da gabata, an dinga kama Yari kan zargin kwashe wasu kudaden Zamfara

FCT, Abuja - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta damke tsohon gwamna Abdulaziz Yari kan binciken da hukumar ke yi game da kudaden da ake zargin akanta janar Ahmed Idris da kwashewa.

Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, an kama shi ne a yammacin Lahadi a gidansa da ke Abuja, kwanaki kadan bayan da yayi nasarar samun tikitin takarar kujerar sanata na Zamfara ta yamma wanda za a yi a shekara ta gaba. Ya yi nasara babu abokin hamayya, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hotuna: Buhari tare da uwargidansa sun dawo Najeriya daga taron da suka halarta a Malabo

Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon gwamna kan zargin hannu a damfarar N80b ta dakataccen AGF
Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon gwamna kan zargin hannu a damfarar N80b ta dakataccen AGF. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ana zargin dakataccen AGF Idris da handamar wasu kudade, lamarin da yasa EFCC ta damke shi tun ranar 16 ga watan Mayu.

Masu bincike na aiki da shugaban kan cewa ana zarginsa da hada kai da wasu wurin satar kudin gwamnati wanda aka damka masa kuma ake tsammanin zai kare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a ciki shi ne Yari, wanda aka kama a yau kamar yadda majiya da hukumar EFCC ta sanar da Premium Times.

Kamar yadda majiyar ta ce, an yi wata harkallar kudi tsaknin Idris da Yari ta wurin naira biliyan 20.

Yari ba sabon shiga bane wurin shiga hannun hukumar EFCC. Ko a shekara da ta gabata, an dinga kama shi tare da tuhumarsa kan zargin waskar da wasu kudaden jihar Zamfara da aka ajiye a banki.

Yari ya yi gwamnan jihar Zamfaa, matalauciyar jihar arewa maso yammacin tsakanin 2007 zuwa 2019. A karkashin mulkinsa ne aka fara samun ta'addanci 'yan bindiga wanda har yanzu suke kai wa yankuna farmaki.

Kara karanta wannan

Sha'aban Sharada na zargin ana shirin tafka magudi a zaben fidda gwani saboda Gawuna

Wani rahoton jihar da wanda ya gaji Yari ya kaddamar, Bello Matawalle, ya zagin Yari da gazawa wurin shawo kan rikicin kabilanci da ke tsakanin yankuna hausawa da Fulani, anda hakan ne ya haifar da 'yan bindiga a yankin.

An ki cin biri, an ci dila: Yadda sabon AGF ke da jikakkiyar tuhumar rashawa da EFCC

A wani labari na daban, Anamekwe Nwabuoku, sabon akanta janar wanda aka nada domin kula da ofishin akanta janar na tarayya, yana da jikakkiyar tuhuma ta zargin rashawa wanda hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ke yi masa.

Idan za a tuna, an nada Nwabuoku ya maye gurbin Ahmed Idris a ranar Lahadi bayan dakatar da Idris da aka yi kuma yana hannun hukumar EFCC kan zarginsa da almundahanar kudi har N80 biliyan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng