Da duminsa: Yan Okada sun kai farmaki rukunin gidaje a Abuja kan kisan abokan aikinsu 2

Da duminsa: Yan Okada sun kai farmaki rukunin gidaje a Abuja kan kisan abokan aikinsu 2

  • Rikici ya barke a birnin tarayya Abuja sakamakon hadarin da ya auku tsakanin mai mota da masu babur biyu
  • Matasa masu aikin Okada sun tuhumci wani mai mota da kashe abokan aikinsu biyu sannan ya gudu
  • Sun kure masa gudu har sai da ya shiga wani rukunin gidaje don mafaka kada su kashe shi

Abuja - Sama da yan babur 100 da aka fi sani da Okada a birnin tarayya sun dira rukunin gidajen Same Global dake unguwar Kabusa don rama kisan abokan aikunsu biyu.

Lamarin ya faru ne lokacin da wani mai mota ya buge masu babur biyu ranar Lahadi kuma ya gudu cikin rukunin gidajen neman mafaka.

Punch ta ruwaito cewa matasan sun bankawa gidaje biyu wuta.

Mazauna rukunin gidajen sun bayyanawa manema labarai cewa yan babur sun far cikin gidajensu ne don fito da mai motar da ya buge yan'uwansu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

An tattaro cewa jami'an tsaro sun dira wajen don kwantar da kuran.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan Okada
Da duminsa: Yan Okada sun kai farmaki rukunin gidaje a Abuja kan kisan abokan aikinsu 2 Hoto: Mobile Punch
Asali: Twitter

Punch tace Shugaban kungiyar mazauna rukunin gidajen ya bayyanawa mata cewa sama da yan babur 100 suka kai farmaki gidajensu.

Yace:

"Suna son kona rukunin gidajen kuma sun kona gidaje biyu. sun balla kofar shiga kuma suka fara jifa cikin gidaje. Mun kasa dakatar da su sai lokacin da yan sanda da Sojojin suka kawo dauki."
"Daga bayan muka samu labarin cewa sun kawo mana hari ne saboda wani mai tuki ya kashe yan babur biyu sai ya gudu cikin rukunin gidajenmu yayinda suka kure masa ido."
"Mutumin da ya bugesu ba mazaunin unguwar bane, kawai ya gudu ciki ne yayinda ya ga akwai ofishin yan sanda cikin rukunin gidajen."

Abuja: Rayuka 5 sun salwanta a arangamar 'yan kasuwa da 'yan achaba

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa EFCC da ICPC ba za su iya gurfanar da deliget a kotu ba

A baya mun ji cewa akalla rayukan wasu mutum biyar ne suka salwanta yayin da gidaje masu yawa suka kone sakamakon arangama tsakanin 'yan kasuwa da 'yan acaba a kwaryar birnin Abuja.

Wani mazaunin yankin ya sanar da Daily Trust cewa, hatsari ne ya ritsa da dan achaba wanda hakan ya janyo tarzoma a yankin.

'Yan kasuwan sun kai wa dan achaban hari bayan sun zarge shi da tukin ganganci wanda ya yi sanadin rasa rayuwar wani fasinja.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel