Buhari Ya Yi Matuƙar Baƙin Cikin Mutuwar Mutane 31 a Wurin Rabon Abinci a Coci a Rivers

Buhari Ya Yi Matuƙar Baƙin Cikin Mutuwar Mutane 31 a Wurin Rabon Abinci a Coci a Rivers

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi bakin cikin mutuwar mutane 31 masu ibada da suka rasu a wurin wani taron coci a Port Harcourt, Jihar Rivers
  • Buhari, ya yi addu'ar Allah ya gafarta wa wadanda suka rasun ya kuma shawarci a rika daukan matakan tsaro yayin shirya duk wani taro
  • Shugaban kasar kuma ya umurci hukumomin bada agaji na kasa su kai dauki ga wadanda suka jikkata sakamakon turereniyar da aka yi wurin taron cocin

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi matukar bakin ciki game da mutuwar mutane da dama da ya faru sakamakon turereniya a wani taron addini a Port Harcourt, Jihar Rivers.

A martanisa kan lamarin, shugaban kasar ya bukaci masu shirya taron addini, siyasa ko wani babban taro su tsara abin yadda ya kamata don kare afkuwar irin mutuwar ko rauni kamar wannan.

Kara karanta wannan

Ka taimaka kada ta tayar damu daga gidajenmu: Mazauna garuruwan dake kan titin Abuja-Kaduna

Buhari Ya Yi Matuƙar Baƙin Cikin Mutuwar Mutum 31 a Wurin Rabon Abincin Coci a Rivers
Shugaba Buhari Ya Yi Matuƙar Baƙin Cikin Mutuwar Mutum 31 a Wurin Rabon Abincin Coci a Port Harcourt. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Buhari ya bayyana hakan ne cikin wani sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi 29 ga watan Mayu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban kasar ya bada umurnin cewa "a yi duk mai yiwuwa don kai wa wadanda suka jikkata ɗauki," kuma hukumomin gwamnati masu bada tallafi ga wanda iftila'i ya faɗa musu su tuntubi gwamnatin Jihar Rivers don tabbatar da cewa sun samu tallafin"

Hakazalika, Shugaban kasar ya mika sakon ta'aziyya ga al'ummar Najeriya da iyalan wadanda suka rasu da Gwamnatin Rivers ya kuma yi addu'ar Ubangiji ya gafarta wa wadanda suka rasun.

Mutum 31 Suka Mutu Yayin Turereniya Wurin Taron Rabon Abinci Da Coci Ta Shirya a Rivers, 'Yan Sanda

Tunda farko, rundunar yan sandan Jihar Rivers ta tabbatar cewa mutane 31 ne suka mutu a turereniyar da aka yi wurin wani taron rabon kyaututuka da kayan abinci a coci da ke Port Harcourt, safiyar ranar Asabar, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Kashe-kashe a Kudu maso Gabas: Ku tsammanci martani mai tsauri daga gareni, Buhari ga 'yan IPOB

Cocin, mai suna Kings Assembly ya gayyaci mambobi ne domin hallartar wani biki inda aka yi alkawari rabon kyautuka da kayan abinci.

Cocin yana kusa da GRA ne a Port Harcourt amma an shirya yin taron ne a Polo Club na Port Harcourt, saboda ana tsammin mutanen da dama za su hallara.

Mukadashiyar kakakin yan sandan Rivers, Grace Iringe Koko ta tabbatar mutum 31 sun rasu, tana mai cewa cocin ta shirya taron ne don raba wa mutane kayan tallafi amma sai abin ya auku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: