Batanci ga Annabi: Sabuwar matsala ta kunno kai a shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara
- Mai magana da yawun Kotunan Musulunci a jihar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya sanar da ɗage zaman shari'ar Sheikh Abduljabbar
- Ya ce ba za'a samu damar zaman Kotun ba yau saboda Alkalin da ke jagorantar Shari'ar ba shi da lafiya, sai 2 ga watan Yuni, 2022
- Gwamnatin Kano ce ta shigar da fitaccen Malamin ƙara bisa zargin yana kalaman batanci da Annabi SAW da tunzura jama'a
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - A ranar Alhamis 27 ga watan Mayu, 2022, Babbar Kotun Kano ta tsara cigaba da sauraron shari'a tsakanin gwamnatin Kano da Sheikh Abduljabbar Kabara.
Sai dai Aminiya ta rahoto cewa wata matsala da ta kunno kai wato rashin lafiyar Alƙalin Kotu, Mai shari'a Ibrahim Sarki Yola, ta janyo tsaiko kuma an ɗage zaman Kotun.
Mai magana da yawun Kotunan Shari'ar Musulunci na jihar Kano, Muzammil Ado Fagge, shi ne ya sanar da haka da ɗage zaman ga manema labarai a Kano.
Fagge ya bayyana cewa bisa haka, Kotu ta ɗage zama kan shari'ar har zuwa ranar 2 ga watan Yuni, 2022, inda za'a dawo a cigaba da sauraron kowane ɓangare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng Hausa ta tataro cewa wannan shi ne na farko da ba za'a zauna Shari'ar Shehin Malamin ba tun bayan gurfanar da shi da gwamnatin Kano ta yi a cikin Watan Yulin 2021.
Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta gurfanar da Malamim ne bisa zargin batanci ga Annabi SAW da kuma tunzura mutane.
Malam Abduljabbar ya rasa lauya
A zaman Kotun da ya gabata, Kotun Musuluncin ta ɗage sauraron ƙarar biyo bayan ficewar lauyan Malam Abduljabbar, inda alƙali ya nemi hukumar taimaka wa shari'a ta baiwa Malamin lauya.
Wannan shi ne karo na uku da Lauyoyin da ke kokarin kare Malamin Addinin Musuluncin suke ficewa daga aikin shari'arsa saboda wasu dalilai.
A wani labarin kuma Kano: Sarki ya tsige wani Dagaci bayan gano yana da hannu a aikata laifi da ya shafi harƙallar filaye
Masarautar Gaya da ke jihar Kano ta tube rawanin Dagacin Gudduba, Mallam Usman Muhd Lawan, da ke yankin karamar hukumar Ajingi a Kano.
Mai Martaba Sarkin Gaya, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, shi ne ya sanar da haka kuma ya ce matakin zai fara aiki ne nan take.
Asali: Legit.ng