Wata mata ta amince ta biya kudi N40,000 don mijinta ya rubuta mata takardar saki
- Wasu ma'aurata da zama ya ki dadi a tsakaninsu har ya kai su ga zuwa gaban kotu don a raba aurensu sun cimma matsaya
- Matar, Hauwa Umar Muhammad ta yarda za ta biya mijinta Umar Zangina kudi N40,000 da ya biya a matsayin sadakin aurenta domin ya bata takardarta ta saki
- Alkalin kotun wanda ya zartar da hukunci, ya ce za a raba auren a duk sanda Hauwa ta gabatar da kudin a gaban sa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Plateau - Wata matar aure mai suna Hauwa Umar Muhammad wacce ke zaune a garin Jos, ta fada ma wata kotu a ranar Laraba cewa ta yarda za ta biya mijinta, Umar Zangina sadakin N40,000 da ya biya na aurenta don a raba aurensu.
Tun farko dai Hauwa ta nemi kotu ta raba aurensu kan hujjar cewa mijin nata baya bata abinci sannan baya iya daukar dawainiyarsu a matsayinsu na iyalinsa, Daily Trust ta rahoto.
Mijin ta hannun lauyansa, I. H. Abdullahi, ya fada ma kotu cewa ba su yi nasarar sulhunta lamarin ba a wajen kotu kamar yadda alkali ya bayar da shawara a farko, don haka ya nemi ta dawo masa da sadakin da ya biya na aurenta.
Alkalin, Ghazali Adam, ya bukaci mai karar ko ta amince za ta biya sadakin inda ta yi na’am da hakan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake zartar da hukuncinsa, alkalin kotun ya fadawa mai karar cewa za a bata takardar sakinta a duk lokacin da ta gabatarwa kotu da kudin.
Zuciyata ta daina ƙaunar mijina, Matar Aure ta nemi Kotun Musulunci ta raba auren
A wani labarin kuma, kotun Shari'ar Musulunci dake zamanta a Anguwar Magajin Gari, Kaduna, ranar Litinin, ta amince da bukatar wata matar Aure, Rakiya Ladan, na raba aurenta bisa hujjar ta dena kaunar mijinta.
Alƙalin Kotun Mai shari'a Nuhu Falalu, shi ne ya gimtse igiyoyin auren wanda ya shafe shekara 9, kamar yadda Jaridar Daily Trsut ta rahoto.
Alƙalin Kotun ya kuma umarci Magidancin mai suna Abba, ya bar matar ta zo ta kwashe karikitanta baki ɗaya daga cikin gidansa.
Asali: Legit.ng