Shugaba Buhari ya samu lambar yabon mai gaskiyan duniya kuma jagoran yaki da rashawa

Shugaba Buhari ya samu lambar yabon mai gaskiyan duniya kuma jagoran yaki da rashawa

  • An alanta shugaba Buhari matsayin mai gaskiya kuma jagoran yaki da cin hancin da rashawa
  • Mai magana da yawunsa yace Buhari ne mutumin farko da aka baiwa wannan lambar yabo a nahiyar Afrika
  • Buhari ya yabawa kungiyar bisa taimakon da suke baiwa hukumomin yaki da rashawa a Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya samu lambar yabon mai gaskiyan duniya kuma jagoran yaki da rashawa.

Kungiyar masu binciken kwa-kwaf na Forensics na Najeriya watau Chartered Institute of Forensics and Certified Fraud Examiners of Nigeria (CIFCFEN) ne suka gabatar masa da wannan lambar yabo.

A cewarsu, sun bashi ne don jinjinawa kokarin da yake yi wajen yaki da rashawa da kuma jajircewarsa wajen yiwa yan Najeriya aiki.

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari ya samu lambar yabon mai gaskiyan duniya kuma jagoran yaki da rashawa Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

2023: Babu ruwan Buhari da shirin ba Jonathan takara a APC inji Fadar Shugaban kasa

A jawabin da mai magana da yawin Buhari, Mr Femi Adesina, ya fitar, ya ce Shugaban majalisar amintattun CIFCFEN, Dr Iliyasu Gashinbaki, ne ya gabatar da lambar yabon ranar Talata a Abuja, rahoton Vanguard.

A cewarsa, babu wanda ake ba wannan lambar yabon illan shugabannin kasashen Afrika masu hali na kwarai.

Yace Shugaba Buhari ne shugaban kasa a nahiyar Afrika na farko da aka ba wannan lambar yabo.

Ya ruwaito shugaba Buhari da cewa:

"Wannan karramawa na kara min karfin gwiwan cewa mu yan kasar nan zamu iya abinda ya dace don kuma kwaikwayon halayen magabatanmu."

Buhari ya jinjinawa mambobin kungiyar bisa kokarin da suke wajen taimakawa kungiyoyin yaki da rashawa irinsu EFCC, CCB, ICPC da hukumar yan sanda.

Buhari ya yi musu alkawarin rattafa hannu kan dokar majalisa dake kan teburinsa wacce ke tabbatar da kungiyarsu a hukunmance.

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

Kara karanta wannan

2023: Da Yardar Allah Ni Da Kai Zamu Fafata a Zaɓen Shugaban Kasa, Tinubu Ya Taya Atiku Murna

Mai bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari na da wanda ya fi son ya gaje shi a 2023, amma ba zai ambaci sunan mutumin ba.

Adesina ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s Politics a jiya Alhamis.

Ya zuwa yanzu dai ministoci Abubakar Malami, Rotimi Amaechi, Godswill Akpabio, Chris Ngige, Ogbonnaya Onu da karamin minista a ma’aikatar ilimi, Emeka Nwajiuba sun shiga takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Adesina, wanda ya ce shi ba dan jam’iyyar APC ba ne mai dauke da katin jam'iyya, ya tabo batun yajin aikin ASUU, da kuma yadda shugaban kasar ke da muradin warware matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng