Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kauyen jihar Katsina

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kauyen jihar Katsina

  • Yayin da ake jimamin abinda yan Boko Haram suka yi wa manoma a jihar Borno, wasu yan bindiga sun sake kai hari Jibiya a Katsina
  • Yan ta'addan sun farmaki manoma a kauyen Gakurɗi da ke yankin Jibiya inda suka kashe aƙalla manoma 15 a gonakin su
  • Haka nan wasu tawagar miyagun na daban sun sace shanu sama da 100 a kauyen Danye Gaba duk a Jibiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Aƙalla manoma 15 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu miyagun yan bindiga suka farmaki ƙauyen Gakurɗi, ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina.

Wannan harin na zuwa ne awanni bayan mayaƙan Boko Haram sun yanka manoma 40 a jahar Borno, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin ƙauyen ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun halaka manoman ne yayin da suke gyaran gonakinsu don shirya wa zuwan Damina.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

Yan bindiga sun kai hari Katsina.
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kauyen jihar Katsina Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce yan bindigan haye a kan Mashina hudu, da farko sun kama hanyar zuwa kauyen Gakurdi, amma da suka ci karo da manoman sai suka buɗe musu wuta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin ya ce:

"Sun zo da misalin karfe 8:30 na safiyar yau Talata a kan Mashin guda hudu, suka fara kashe mutanen, mutum uku suka mutu a gona ɗaya, amma a hankali aka gano su 15 aka kashe a gonaki daban-daban."

Ya ƙara da cewa zuwa lokacin da mutanen ƙauyen suka ankara da abun da ke faruwa, maharan sun gama ta'addancin sun tsere.

Yan bindiga sun sace dabbobi a wani kauye daban

A wani cigaban, yan bindigan daji sun yi awon gaba da shanu sama da 100 a kauyen Danye Gaba, gundumar Bugaje duk a yankin Jibiya.

Ƙauyen da wannan harin na biyu ya auku ba shi da wani nisa tsakaninsa da sansanin sojoji na 17 da ke jihar Katsina, tsakanin su kilo mita biyu ne kacal.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi ajalin mahaifiya da 'ya'yanta hudu, sun haɗa da wasu mutum biyu

Wani mazauni da ya nemi a sakaya sunansa ya ce shanun da maharan suka sace na wasu mutane ne kusan Bakwai, kuma lamarin ya faru ne da karfe 1:30 na dare.

Ya ce tun da karfe 8:00 suka fahimci motsin yan ta'addan kuma suka ankarar da hukumomin tsaro amma ba bu wani mataki da suka ɗauka har suka aikata nufin su.

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, don tabbatarwa ya ce, "Yanzu haka suna tare da kwamishina domin gano halin da ake ciki."

A wani labarin kuma Yan bindiga sun buɗe wa motar ɗan takarar APC wuta a Borno, rayuka sun salwanta

Wasu m iyagun yan bindiga sun mamayi jerin gwanon ɗan takarar Sanata a APC, sun buɗe musu wuta da safiyar Lahadi a Borno.

Rahoto ya nuna cewa yan sanda biyu sun rasa rayukan su yayin da wasu magoya baya da dama ke kwance a Asibiti sanadin harin.

Kara karanta wannan

Tambuwal da Gwamnoni 9 masu neman mulki su na kashe miliyoyi duk rana a hayar jirgi

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262