An kewaye ni ta ko ina, Rochas Okorocha ya yi martani bayan Jami'an EFCC sun mamaye gidansa
- Sanata Rochas Okorocha ya yi martani da cewa jami'an EFCC sun mamaye gidansa gaba da baya amma ba zai fasa abinda ya shirya ba
- Tsohon gwamnan na jihar Imo ya ce kamata ya yi ace ya na shirin zuwa wurin tantance yan takarar shugaban ƙasa na APC
- A dazu ne, jami'an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'adi suka kewaye gidan Sanatan da nufin damƙe shi
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya maida martani kan mamaye gidansa na Maitama da Jami'an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta'annati (EFCC) suka yi a Abuja.
Okorocha, wanda ke fafutukar samun tikitin takarar shugaban ƙasa a APC, ya shaida wa Channels tv cewa an yi garkuwa da shi a harabar gidansa.
Idan ba'a amsa bukatunmu ba, ba za'a sake amfani da jirgin kasa da titin Abuja-Kaduna ba: Yan ta'adda
Okorocha ya tabbatar da cewa:
"Ina karkashin garkuwa zan iya cewa dakarun EFCC sun mamaye gidana ta ko ina gaba da baya, na nemi bayani kan idan suna da izinin kama ni amma shiru, kamata ya yi ace yanzu ina shirin tantancewa."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ban san dalilin da yasa hakan take faruwa ba kuma bisa rashin sa'a ya na faruwa anan (Gidana)."
Haka ba zai hana ni taron da na kira ba - Okorocha
Sanatan ya kara da cewa shirinsa na gaba shi ne taron manema labarai, kuma zuwan dakarun EFCC ba zai hana yan jarida shiga harabar gidansa ba.
"Ina shirin bayyana gaban manema labarai, tabbas EFCC ba zata dakatar da yan jarida zuwa gidana ba. Sun shigo harabar gidana amma yan jarida zasu zo su yi hira da ni, ba zasu hana su ba."
Yayin da aka tambaye shi ko zai miƙa kansa ga EFCC, Okorocha ya ƙara da cewa:
"Zan cigaba da zama anan har sai na san abinda ke wakana saboda wannan abu ne na gaske, ina son ganin takardar izinin kamu ko umarnin Kotu."
Tun da farko mun kawo muku cewa Jami'an EFCC sun mamaye gidan ɗan takarar shugaban kasa a APC zasu kama shi
Jami'an hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasa ta'adi, (EFCC) sun mamaye gidan tsohon gwamnan Imo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, Rochas Okorocha.
Tawagar dakarun hukumar EFCC ɗin sun dira gidan tsohon gwamnan da ke yankin Maitama a babban birnin tarayya Abuja da nufin kama shi.
Asali: Legit.ng