Da Duminsa: Jami'an EFCC sun mamaye gidan ɗan takarar shugaban kasa a APC zasu kama shi

Da Duminsa: Jami'an EFCC sun mamaye gidan ɗan takarar shugaban kasa a APC zasu kama shi

  • Dakarun EFCC sun yi dirar mikiya a gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha da ke birnin tarayya Abuja
  • Rahoto ya nuna cewa jami'an EFCC sun manaye gidan ta ko ina, sun nemi a ya miƙa kansa ko kuma ya amsa gayyata zuwa ofishin su
  • Okorocha, wanda ke fafutukar neman tikitin takarar shugaban ƙasa APC, ya ce ba inda zai je har sai sun gabatar masa da izinin kamu

Abuja - Jami'an hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasa ta'adi, (EFCC) sun mamaye gidan tsohon gwamnan Imo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, Rochas Okorocha.

Tawagar dakarun hukumar EFCC ɗin sun dira gidan tsohon gwamnan da ke yankin Maitama a babban birnin tarayya Abuja da nufin kama shi.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Muka Yi Dirar Mikiya a Gidan Okorocha, EFCC Ta Magantu

A wani Bidiyo da Channels tv ta samu, an hangi Jami'an hukumar sun mamaye ilahirin harabar gidan tsohon gwamnan.

EFCC ta mamaye gidan Okorocha na Abuja.
Da Duminsa: Jami'an EFCC sun mamaye gidan ɗan takarar shugaban masa a APC zasu kama shi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jami'an sun jaddada cewa ya kamata Okorocha, wanda ke neman tikitin takarar shugaban ƙasa karkashin APC, ya miƙa kansa ko kuma ya girmama gayyatar da EFCC ta masa da daɗewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka nan kuma Jami'an sun bayyana cewa ba zasu bar ko mutum ɗaya daga cikin iyalan gidan Okorocha ya fita ba har sai sun miƙa musu tsohon gwamnan.

Bayanai sun nuna cewa Dakarun hukumar yaƙi da cin hancin sun rinka bincikar duk wanda ya zo da nufin shiga ko fita daga harabar gidan Sanata Okorocha.

Sun kuma gargaɗi jami'an hukumar yan sanda da ke aiki a gidan ɗan takarar na APC da su fice su bar harabar gidan a yanzu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan EFCC ta kewaye gidansa, Rochas Okorocha ya faɗi gaskiyar halin da yake ciki da mataki na gaba

Martanin Okorocha

Da yake martani kan lamarin, tsohon gwamnan na jihar Imo ya ce jami'an hukumar EFCC sun tsare shi tamkar garkuwa a gidansa.

Ya kuma yi Allah wadai da yunkurin na kama shi, tare da alwashin ba zai fito ba har sai ya ga takardar izinin kamu.

"An yi garkuwa da ni anan, na nemi idan sun samu izinin kama ni ne amma shiru, kamata ya yi ace ina shirye-shiryen tantance yan takara na APC." inji shi.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kauyen jihar Katsina, sun kashe manoma 15

Yayin da ake jimamin abin da yan Boko Haram suka yi wa manoma a jihar Borno, wasu yan bindiga sun sake kai hari Jibiya a Katsina.

Yan ta'addan sun farmaki manoma a kauyen Gakurɗi da ke yankin Jibiya inda suka kashe aƙalla manoma 15 a gonakin su.

Kara karanta wannan

Har yanzu ina APC, ban koma PDP ba: Sanata Danjuma Goje

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262