Matasa sun lallasa shugaban hukumar kwallo bayan fadi caca N5m, sunce sayar da wasan yayi

Matasa sun lallasa shugaban hukumar kwallo bayan fadi caca N5m, sunce sayar da wasan yayi

  • Shugaban hukumar wasanni a jihar Oyo ya sha da kyar hannun matasa a filin kwallo a garin Ibadan
  • Matasa masu goyon kungiyar 3SC sun nuna fushinsu kan rashin samun nasara a wasan, sun ci 1-0 amma aka rama a minti na 92
  • Adesuwi ya je kallon wasan kwallo ne amma matasan suka zargesa da cewa ya sayar da wasan kuma yanzu sun yi asarar milyan 5 na caca

Ibadan - Shugaban hukumar wasannin jihar Oyo, Gbenga Adewusi, ya sha duka hannun matasa bayan an tashi wasan kwallo kunnen jaki tsakanin kungiyar Shooting Stars Sports Club (3SC) da MFM Football Club.

An buga wasan ne a filin kwallon Lekan Salami dake Ibadan, birnin jihar Oyo.

Kungiyar gwallon 3SC ta zura kwallo daya ragar MFM a minti na 42 amma aka rama a minti na 92.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama yan yankan aljihu 10 a wajen zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP

Adesuwi ya bayyanawa manema labarai cewa matasan sun jibgesa ne saboda zargin cewa ya sayar da wasan.

Shugaban hukumar kwallo
Matasa sun lallasa shugaban hukumar kwallo bayan fadi caca N5m, sunce sayar da wasan yayi Hoto: Punch
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace matasan sun tuhumesa da ja musu asarar milyan biyar a cacan da sukayi kan wasar.

Yace:

"Na je filin kwallo don kallon wasar 3SC da MFM, inda aka tashi 1-1. Wasu masoyan 3SC suka kai min hari bayan wasan."
"Suna zargina da cewa na sayarwa MFM wasar..kuma na ja musu asarar N5m a cacar yanar gizo."
"Fusatattun matasan sun jibge ni har na kusa mutuwa."

A hoton da Punch ta dauka, matasan sun fasawa Adewusi fuska kuma an garzaya da shi asibiti.

Kungiyar kwallon Lyon ta sallami dan wasa don barka tusa a bainar jama'a

Kungiyar kwallon Olympique Lynonnais dake kasar taka leda a Ligue 1 a Faransa ta sallami dan wasanta, Marecelo, bayan barka tusa a dakin shiryawan yan kwallo kuma ya fara dariya.

Kara karanta wannan

Halin da Atiku, Saraki, Tambuwal, da Wike suke ciki a wajen zaben zama ‘dan takaran PDP

Lyon a watan Agustan da ya gabata cewa an dakatad da dan kwallon kuma an rage masa matsayi bisa dabi'ar da bai dace ba.

A cewar L'Equipe, Marcelo dan shekaru 34 ya barka tusa ne bayan wasa da kungiyar Angers, inda Lyon ta sha kashi kuma Marcelo yaci gida "Own Goal" a wasar.

An ruwaito cewa bayan fushin da ake da shi bisa cin gidan da yayi, ya barka tusa a dakin 'dressing room' sannan kuma ya fara dariya.

Diraktan harkokin horo na kungiyar, Juninho ya dakatad da Marcelo. Daga baya kuma aka sallamesa a watan Junairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel