Siyasa: 'Yan daba sun farmaki 'yan jarida a taron kamfen din wani gwamnan APC
- Rahoton da muke samu daga Kudu maso Yammacin kasar nan ya shaida cewa, 'yan daba sun farmaki tawagar kamfen na gwamna
- An ce tsagerun sun raunata wasu 'yan jarida ciki har shugaban kungiyar 'yan jarida na jihar ta Osun a jiya Litinin
- Ya zuwa yanzu, an ruwaito cewa, akwai akalla mutum biyu da aka zarce dasu asibiti domin duba lafiyarsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Osun - ’Yan daba sun kai hari kan motocin da ke dauke da ‘yan jarida a lokacin da suke fitowa daga taron kamfen din gwamnan Osun, Gboyega Oyetola a Gbongan, karamar hukumar Ayedaade ta jihar a ranar Litinin.
Oyetola dai ya gama yi wa magoya bayansa jawabi ne a Unguwar Arapajo da ke Gbongan lokacin da aka kai wa ‘yan jarida hari, inji Premium Times.
Maharan sun yi amfani da kulake, layu, duwatsu, da gatari wajen fasa gilasan motocin da ke dauke da ‘yan jaridan inda suka jikkata hudu daga cikinsu.
Wasu mutanen da ke cikin motar sun hada da shugaban kungiyar ‘yan jarida (NUJ) reshen Osun, Mista Shina Abubakar da wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Mista Victor Adeoti, da sauran ‘yan jarida, rahoton The Guardian.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A halin da ake ciki, kwamishinan yada labarai, Funke Egbemode, ta dauki biyu daga cikin ‘yan jaridan da ‘yan daban suka raunata zuwa asibiti domin yi musu magani.
Abin da ya faru a taron kamfen
Oyetola dai ya fara kamfen ne a Orileowu da ke karamar hukumar, inda ya yi jawabi ga magoya bayan jam’iyyar kafin ya koma Gbongan.
Ya shaida wa magoya bayansa a Gbongan cewa ayyukan da ya yi a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata shaida ce ta zurfin akidarsa na kawo ci gaba.
Gwamnan ya sake nanata cewa yana cikin gwamnati ne don yin hidima ga jama'a kuma ya yi kira ga ‘yan jihar Osun da su mara masa baya da burinsa na “gyara” jihar.
Neja: 'Yan Sanda Sun Kama Wani, Lawan Abubakar, Kan Yunƙurin Tono Gawa a Maƙabarta
A wani labarin, rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta yi ram da Lawal Abubakar, dan shekara 16, wanda mazaunin Kasuwan-Gwari ne da ke cikin Minna, inda su ke zarginsa da yunkurin tono wata gawa daga kabarinta a makabartar Chanchaga.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a ranar Litinin, DSP Wasiu Abiodun ya bayyana hakan a wata tattaunawa da su ka yi da wakilin NAN a Minna.
Kamar yadda ya shaida: “Da misalin karfe 10:20 na safiyar Asabar, jami’an ‘yan sanda na ofishin Chanchaga su ka kama wani Lawali Abubakar, mazaunin Kasuwan-Gwari da ke Minna.
Asali: Legit.ng