Amma dai tela bai kyauta ba: Dinkin rigar wani yaro ya girgiza intanet, ana ta cece-kuce

Amma dai tela bai kyauta ba: Dinkin rigar wani yaro ya girgiza intanet, ana ta cece-kuce

  • Wani karamin yaro ya sha wani kalan dinkin rigar makarantarsa daga tela, inda aka ga alama telan bai gwada shi ba kafin dinkin
  • Rigar ta makarantar ta yi matukar girma sosai kuma a haka yaron ya ke ta faman tafiya da ita duk da ta lullube kafafunsa
  • Jama'a a kafofin sada zumunta sun mayar da martani kan faifan bidiyon yaron sanye da kayan, inda da dama ke cewa yaron zai iya amfani da shi har ya kammala makaranta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Wani yaro dan Najeriya ya samu doguwar rigar makaranta da ta girme shi daga telansa, lamarin da ya girgiza da yawan jama'a a kafafen sada zumunta.

Lokacin da bidiyon ya fito a intanet, ya sa masu amfani da shafukan sada zumunta suna magana tare da wasu da ke cewa abu ne na da aka saba a ba yara manyan tufafi a kasar nan.

Kara karanta wannan

Dankwali ya ja hula: Bidiyon wata amarya yayin da take yiwa angonta budar kai ya janyo cece-kuce

Yadda tela ya rikita kayan makarantar yaro
Amma dai tela bai kyauta ba: Dinkin rigar wani yaro ya girgiza intanet, ana ta cece-kuce | Hoto: @dabod_speed
Asali: Twitter

Bidiyon da ya yi ta yawo a intanet ya nuna lokacin da yaron ke kokarin tafiya da kyar a cikin rigar burm-burm saboda ta kai har ga kafafunsa.

Yaron an ga ya fadi kasa a cikin faifan bidiyon da @dabod_speed ya yada, watakila saboda girman rigar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan soshiyal midiya

@OlibeJ ya ce:

"Zai girma a ciki."

@A_deoye yayi sharhi da cewa:

"Wannan yana da matukar tasiri ga tattalin arziki idan za ku tambaye ni. Babu batun dinka rigar makaranta har zuwa aji uku, kuma idan Ethan ba shi da tsawo, zai saka ta har aji shida, kun ga lamari ne mai matukar riba."

@favourite_meal ya ce:

"Wasu na saka riga suna zuwa makaranta amma dan uwanku ya saka jallabiya kamar yadda babban mutum ke yi, abin da ya rage yanzu sai siyan wannan abin ka na dubai a daura masa a ka sai ya zama cikakken balarabe kawai."

Kara karanta wannan

CAN: Ana amfani da sunan zagin Annabi domin kashe Kiristoci a Arewa

@ugo_prisca ya ce:

"Ku dan soka rigar cikin wandonsa mana, ko ku yi amfani da allura da zare a rage shi, yayin da yake girma, sai ku ke kara tsawon, sai ka ce ba ku karanta tattalin gida a makaranta ba."

Cakwakiya: Wata mata ta ba da labarin yadda ta auri yayanta har suka haifi 'ya'ya 4

A wani labarin, wata mata mai suna Domitila ta ce ta auri dan uwanta cikin rashin sani saboda bata taba sanin tana da yaya ba.

Kamar yadda labarin ya nuna, iyayensu sun yi watsi da su ne tun suna kanana kuma a haka suka watsu a wurare daban-daban babu mai kula da su.

Babu daya daga cikin ’yan’uwan biyu da ya san cewa suna da dangantaka domin ba su girma tare ba duba da yadda iyayensu suka watsar dasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.