Da duminsa: Buhari ya dira a birnin Abuja bayan ta'aziyyar kwana 2 da ya je UAE
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a birnin tarayya na Abuja bayan ziyarar kwanaki biyu da ya kai Abu Dhabi, UAE
- Ya kai ziyara tun ranar Alhamis inda ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Khalifa tare da taya sabon shugaban kasar murna
- Buhari wanda ya samu rakiyar wasu daga cikin ministocinsa ya bayyana fatansa na cewa Najeriya da UAE za su cigaba da tabbatar da alakar da ke tsakaninsu
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iso Abuja bayan ziyarar kwanaki biyu da ya kai Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE.
Shugaban kasan wanda ya bar Najeriya a ranar Alhamis, ya dira a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja wurin karfe 4 na yamma tare da tawagar da suka masa rakiya, Daily Trust ta ruwaito.
A birnin Abu Dhabi, shugaban kasa Buhari ya gana da sabon shugaban kasa UAE, Mai martaba Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, wanda ya mika wa gaisuwa bisa rashin tsohon shugaban kasa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan da aka yi.
Channels TV ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammad Buhari ya jera da sabon shugaban kasan inda suka yi sallar Juma'ah tare sannan aka yi wa tsohon shugaban kasar UAE, Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan addu'o'i.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin takaitacciyar ganawa da Sheikh Zayed Al Nahyan, sabon shugaban kasar UAE, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyarsa da ta Najeriya kan rashin Sheikh Khalifah kuma ya taya sabon shugaban kasan murnar hayewa karagar mulkin.
Shugaban Buhari ya bayyana fatansa na cewa karkashin mulkin Sheikh Mohamed, kasashen biyu za su cigaba da hada kai wurin tabbatar da tsaro, yaki da ta'addanci, dabbaka cinikayya da kuma kawo cigaba mai dorewa.
Shugaban kasan ya samu rakiyar karamin ministan lamurran harkokin waje, Ambasada Zubairu Dada, ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ministan babban birrnin tarayya, Mohammed Bello da Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika.
Sauran mutanen da ke cikin tawagar sun hada da mai bada shawara kan tsaron kasa, Manjo Janar Mohammed Monguno mai ritaya da Darakta janar da hukumar binciken sirri, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.
Asali: Legit.ng