Nan Ba Da Daɗewa Ba Za a Dena Ganin Takardar Naira a Najeriya, Babban Bankin Najeriya, CBN
- Nan da kankanin lokaci yan Najeriya za su fara neman takardar naira da suka kashe kashewa a gari su rasa, don haka ake shawartar mutane su rungumi e-Naira
- Mr Godwin Okafor, kwantrola na CBN reshen Jihar Delta ne ya bayyana hakan yayin wayar da kan yan kasuwa kan amfani da e-Naira
- Dr Aminu Bizi, kwararre kan e-Naira ya ce CBN na asara wurin buga naira, sannan e-Naira ta fi tsaro kuma babu caji kamar POS da ATM
Delta - Babban Bankin Najeriya, CBN, ta ce nan ba da dadewa za a nemi naira ta takarda a rasa, yana mai shawartar mata da maza yan kasuwa su yi rajista da e-Naira.
The Punch ta rahoto cewa kwantrola na CBN reshen Jihar Delta, Mr Godwin Okafor, ne ya furta hakan a ranar Juma'a a fitaccen kasuwar Ogbogonogo yayin wayar da kan yan kasuwa game da e-Naira.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bukaci yan kasuwan su shiga tsarin babban bankin Najeriya na e-Naira.
Ya ce:
"Mun zo nan kasuwa ne domin wayar da kan mutane game da amfani da e-Naira. CBN ta amince da shi, ba kamar Bitcoin da doka bata amince da shi ba."
Kwararre kan e-Naira ya bayyana fa'idar ta ga al'umma
Kwararre na CBN kan e-Naira, Dr Aminu Bizi, ya ce an zabi Delta a matsayin jiha ta biyu domin wayar da mata yan kasuwa kan e-Naira bayan Jihar Legas.
"Mun zo nan ne domin wayar da kan maza da mata yan kasuwa, shago zuwa shago kan amfani da e-Naira. CBN ta wuce da batun ATM, POS, don haka za mu wayar da kan yan acaba/adaidaita kan wannan sabon tsarin.
"Nan da kankanin lokaci za a dena ganin takardar Naira domin CBN na kashe kudi don buga ta kuma mutane suna cin zarafinta a kasuwa, liki wurin biki/taro, biyan yan acaba/adaidaita da sauransu, CBN na asara."
Ya ce e-Naira yana da dadin amfani, babu caji kamar ATM ko POS kuma ba za a iya mata kutse ba.
A jawabinsa, sakataren gwamnatin jihar, Cif Patrick Ukah, ya yaba wa CBN bisa bullo da tsarin na e-Naira.
Asali: Legit.ng