Kotu ta yankewa Bature hukuncin kisa kan laifin kashe matarsa Zainab da 'yarsa a Legas

Kotu ta yankewa Bature hukuncin kisa kan laifin kashe matarsa Zainab da 'yarsa a Legas

  • Bayan kimanin shekaru uku ana shari'a a Kotu, an yanke hukunci kan Baturen da ake zargi da kisar matarsa da diyarsa
  • Kotu jihar Legas ta tabbatar da zargin da ake yiwa Dane kuma ta yanke masa hukunci kisa ta hanyar rataya
  • A Najeriya, akwai dokar kashe mai laifi ta hanyar rataya amma gwamnoni ba su aiwatar da wannan doka

Legas - Wata babbar kotun jihar Legas a ranar Juma'a, ya yankewa wani bature dan kasar Denmark, Dane Peter Nielsen, hukuncin kisa bisa laifin kashe matarsa 'yar Najeriya da diyarsa.

Alkali Bolanle Okikiolu-Ighile ya yankewa Dane hukuncin kisan ta hantar rataya ne sakamakon shari'ar da akayi wanda gwamnatin jihar Legas ta shigar kansa. Kamfanin dillancin labarai NAN ta bayyana.

An tuhumi Dane da laifin kashe matarsa mai suna Zainab, da diyarsu yar shekara uku mai suna Petra, a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Gwamna ya saka tukwicin naira miliyan 10 kan makasan dan majalisa a jaharsa

Gwamnatin jihar tace Dane ya hallaka Zainab da Petra ne misalin karfe 3:45 na dare cikin gida mai lamba No. 4, Flat 17, Bella Vista Tower, Banana Island, Ikoyi, jihar Lagos.

An gurfanar da shi ranar 13 ga Yuni, 2018.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bature
Kotu ta yankewa Bature hukuncin kisa kan laifin kashe matarsa Zainab da 'yarsa a Legas Hoto: TheNation
Asali: Facebook

Kotu Bada Umurnin a Tsare Matashi, Ɗanladi, Da Ya Kashe Abokinsa Saboda Ya Nemi Budurwarsa

Wata kotun majistare da ke zamanta a Akure ta bada umurnin tsare wani mutum mai shekara 22, Money Danladi, kan zargin kashe abokinsa da wuka, Sunday Babaji, saboda fadakan budurwa.

Mai gabatar da kara, Sufeta Nelson Akintimehin ya shaida wa kotu cewa Danlami ya aikata laifin ne a ranar 9 ag watan Mayun 2022, misalin karfe 9 na dare a Badokun Camp via Ode-Aye, karamar hukumar Okitipupa a jihar.

A cewarsa, wanda ake zargin ya daba wa abokinsa mai shekara 25, Sunday Babaji, wuka ya kashe shi saboda rikici da ya shiga tsakaninsu kan wata budurwa.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: