Saudiyya Ta Bai Wa Marayu 1,960 Tallafin Naira Miliyan 113 a Jihar Kebbi

Saudiyya Ta Bai Wa Marayu 1,960 Tallafin Naira Miliyan 113 a Jihar Kebbi

  • Kungiyar Tallafin Kasa da Kasa ta Musulunci, IIRO, ta Masarautar Saudi Arabia, ta bai wa marayu 1,960 tallafi N131 a Jihar Kebbi ranar Juma’a
  • Yayin gabatar da shirin a masaukin shugaban kasa da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Gwamna Atiku Bagudu ya nuna farincikinsa ga IIRO akan karamcinsu
  • Gwamnan wanda ya samu wakilcin Babale Umar-Yauri, Sakataren Gwamnatin Jihar, SSG, ya ce gwamnatin jihar ta lashi takobin shiga gaba-gaba akan duk wasu al’amuran marayun

Jihar Kebbi - A ranar Juma’a, Kungiyar Tallafin Kasa da Kasa ta Musulunci, IIRO, na Masarautar Saudi Arabia ta tura Naira miliyan 131 ga marayu 1,960 da ke Jihar Kebbi, The Guardian ta ruwaito.

Yayin kammala shirin wanda aka yi a masaukin shugaban kasa da ke Birnin Kebbi, Gwamna Atiku Bagudu ya mika godiyarsa akan karamcin da aka yi musu tare fatan ci gaban shirin.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

Saudiyya Ta Bai Wa Marayu 1,960 Tallafin N113m a Jihar Kebbi
Kasar Saudiyya Ta Bai Wa Marayu 1,960 Tallafin N113m a Jihar Kebbi. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

NAN ra ruwaito cewa an tura kudin ne ta ofishin kungiyar musuluncin da ke Jihar Kaduna.

Gwamnan ya lashi takobin tallafawa marayun jihar iyakar iyawarsa

Sakataren Gwamnatin Jihar SSG, Babale Umar-Yauri wanda ya wakilci gwamnan, ya tabbatar da cewa mulkinsu ya yi matukar mayar da muhimmanci akan marayu.

Yayin da ya lura da yadda kungiyar ta dage wurin tallafi da kuma ilimantar da marayu a fadin duniya, Bagudu ya kuma yaba wa gwamnatin jihar akan nata kokarin.

A cewarsa:

“Za mu yi iyakar kokarinmu wurin bai wa IIRO goyon baya har ta kai ga gaci da samun tarin nasarori, za mu taimaka wurin cikashe bangarorin da akwai gurabu na bukatun marayun.
“Ina son yin amfani da wannan damar wurin rokon masu hannu da shuni akan taimakawa marayu don samar musu da kyakkyawar rayuwa.”

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Saudiyya Ta Bai Wa Marayu 1,960 Tallafin N113m a Jihar Kebbi
Kasar Saudiyya Ta Bai Wa Marayu 1,960 Tallafin N113m a Jihar Kebbi. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Ya yaba wa sarakunan gargajiyan Kebbi akan kokarinsu

Ya kara da yaba wa Sarakuna kamar na Gwandu, Muhammad Iliyasu-Bashar, Argungu, Muhammad Sama’ila-Mera da na Zuru, Mohammed Sani-Sami akan kokarinsu wurin taimaka wa marayu kamar yadda Daily Nigerian ta nuna.

A jawabin shugaban shirin ilimin kungiyar ta Musulunci, IIRO, na ofishin Kaduna, Dr Tahir Baba-Ibrahim ya ce ba musulmai kadai su ke tallafawa ba, har da duk wani maraya na ko wanne addini a fadin duniya.

Ya bukaci marayun da su ka amfana da shirin da su kasance masu hakuri da sabuwar dokar kungiyar wacce aka kafa da za a dinga biyansu sau hudu a ko wacce shekara.

Baba-Ibrahim ya mika godiyarsa ga gwamnatin Jihar Kebbi akan karamcinta da kuma taimako wurin ganin ci gaban shirin.

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A wani rahoton, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kara karanta wannan

Kisan Deborah: Kungiya ta nemi a kamo limamin BUK bisa zargin halasta jinin Bishop Kukah

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164