Ana Zaman Ɗar-Ɗar Yayin Da Tsohon Shugaban APC Na Bauchi Ya Mutu Cikin Yanayi Mai Ɗaure Kai

Ana Zaman Ɗar-Ɗar Yayin Da Tsohon Shugaban APC Na Bauchi Ya Mutu Cikin Yanayi Mai Ɗaure Kai

  • Mutuwar tsohon shugaban APC na karamar hukumar Bauchi, Alhaji Musa Gwabba ta sanya wa mutane alamar tambaya mai yawa musamman ganin yadda aka kasa gane silarta
  • Ya rasu ne a ranar 14 ga watan Mayu yana da shekaru 62 bayan an gan shi a mawuyacin yanayi a dakin wani otal da ke Bauchi, daga nan aka garzaya asibiti da shi
  • Sai dai ko da aka kai shi asibiti, likita ya tabbatar da mutuwarsa wacce yanzu haka ake kan tuhumar mutane uku dangane da lamarin, har ila yau asibiti su na kan binciken gawarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bauchi - Mutuwar ba zata da shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Bauchi, Alhaji Hussaini Musa Gwabba ya yi ta bar mutane cike da tunanin sila da kuma wadanda ke da hannu akai.

Kara karanta wannan

Rudani: 'Yan bindiga sun sako hakimin kauyen Kano, sun rike farfesan da ya kai kudin fansa

Daily Trust ta ruwaito cewa Gwabba ya rasu ne a ranar 14 ga watan Mayu yana da shekaru 62 da haihuwa, kuma har yanzu an kasa gane silar mutuwarsa.

Ana Zaman Ɗar-Ɗar Yayin Da Tsohon Shugaban APC Na Bauchi Ya Mutu Cikin Yanayi Mai Ɗaure Kai
Tsohon Shugaban APC Na Bauchi Ya Mutu Cikin Yanayi Mai Ɗaure Kai. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Ahmed Wakil ya shaida, wasu mutanen kirki ne su ka bayyana yadda su kagan shi a mummunan yanayi cikin wani daki da ke Otal din Khairan.

An kama mutane 3 da ake zargin su na da masaniya

Kamar yadda Wakil ya shaida bisa ruwayar Daily Trust:

“Har DPO din Ofishin ‘yan sandan yankin sai da ya je har Otal din Khairan da ke kusa da Asibitin Kwararru a Bauchi, inda ya gan shi yana ta amai daga nan aka zarce da shi asibiti. Anan ne likita ya tabbatar da cewa ya mutu.
“Binciken ya janyo an kama mutane uku wadanda yanzu haka su ke shan tambayoyi.”

Kara karanta wannan

Shekara da mutuwar Shekau: Waiwaye ga hare-haren Boko Haram 12 da suka girgiza duniya

Yanzu dai ana kan jiran sakamakon asibiti don sanar da mutane gaskiyar abinda aka gano duk da dai zai dauki lokaci.

Sai dai mutuwar ta shi ta janyo tarin tambayoyi yayin da makusantansa su ke ta zargi iri-iri. Akwai wadanda su ke ganin guba abokan hamayyarsa na siyasa su ka zuba masa a abinci.

Dama ana ta barazana ga rayuwarsa

Su na wannan zargin ne saboda kowa ya san yadda marigayin ya kasance mutum mai son zaman lafiya don ba ya da abokin fada.

Sun yi zargin an halaka shi ne saboda alakarsa ta kusanci da tsohon gwamnan jihar, Mohammed Abubakar, wadanda abokan hamayyarsa su ka lashi takobin ba zai koma a matsayin gwamnan jihar ba.

Wasu mutane sun yi zargin an halaka shi ne bayan an dinga yin barazana ga rayuwarsa, wanda hakan ya sa ya bar gidansa zuwa otal din don ya boye wa masu yunkurin halaka shi.

Kara karanta wannan

Batanci: Ku girmama addinin mutane da abinda suka yi imani da shi sai a zauna lafiya, El-Rufa'i

Sun ce iyalansa sun san inda ya ke don har abinci su ke kai masa a inda ya boye.

Yayin da aka tambayi wakilin iyalansa, Dr Bala Gambo Jahun, ya ce ba za su ce komai ba dangane da silar mutuwarsa har sai sun ji sakamakon binciken ‘yan sanda.

Iyalansa su na bukatar tallafi

A cewarsa, sun yarda da cewa kowa sai ya mutu wata rana, kuma duk wanda ya halaka dan uwansu zai koma ga mahaliccinsa wata rana.

“Muna fatan Ubangiji ya yafe masa kurakurensa ya kuma saka masa da Jannatul Firdausi,” a cewarsa.

Tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, a wata takarda da hadiminsa ya saki, Abubakar Gabi, ya ce duk da dai ba a gujewa mutuwa amma ba za a bar batun a haka ba kawai saboda siyasa.

Ya yi kira akan a yi bincike mai yawa don gano wanda ya ke da hannu akan mutuwar tsohon shugaban.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

A cewarsa zai yi aiki tukuru tare da manyan lauyoyi don tabbatar da mai laifin ya fuskanci fushin hukuma.

Shugaban jam’iyyar APC na wata gunduma da ke karamar hukumar Bauchi, ya yi kira ga ‘yan takarar gwamna guda 9 na APC da su taimaka wa iyalan mamacin musamman ganin ko gidan kansa ba ya da shi, iyalansa a gidan haya su ke zama.

Daya daga cikin ‘yan takarar, Alamin Sani Muhammad, ya bukaci mutane su kwantar da hankali su kuma su bar jami’an tsaro su yi aikinsu, sannan ya ce zai yi iyakar kokarinsa wurin tallafawa iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164