Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Dubai gaisuwar ta'aziyyar Sarkin UAE da ya rasu

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Dubai gaisuwar ta'aziyyar Sarkin UAE da ya rasu

  • Shugaban kasan Najeriya zai tafi kai gaisuwar ta'aziyyya hadaddaiyar daular Larabawa bisa rasuwar shugaban kasansu
  • Fadar shugaban kasa ta bayyana muhimmancin wannan tafiya ga alakar dake tsakanin Najeriya da Dubai
  • Shugaban kasan zai samu rakiyan wasu Ministocinsa da hadimai makusanta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar UAE don gaisuwar ta'aziyyar rasuwar tsohon Sarki Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan da ya rasu farkon makon nan.

Shugaban kasan ba zai dawo Najeriya ba sai ranar Asabar.

Hadimin sashen gidajen talabijin da rediyo na shugaban kasa, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

Yace:

Shugaba Muhammadu Buhari zai gana da sabon shugaban kasar UAE Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, don amsa ta'aziyyar mutuwar tsohon shugaban AbuDhabi Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan."
An sa ran Shugaban kasan ya dawo ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yan kasar Nijar, da wasu yan bakin haure ke aikin Okada a Legas, Kwamishanan yan sanda

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya rasu yana da shekaru 73, Khaleej Times ta ruwaito.

Wata sanarwar da kamfanin dillacin labarai ta WAM ta yada a Twitter ta ce:

"Ma'aikatar Harkokin Shugaban Kasa ta sanar da cewa za a yi zaman makoki na kwanaki 40 a hukumance tare da sauke tutoci da kuma rufe ma'aikatu da hukumomin gwamnati a matakin tarayya da na kananan hukumomi da kuma kamfanoni masu zaman kansu."

Sheikh Khalifa, wanda yasha fama da rashin lafiya tsawon shekaru da dama, ya dade da daina shiga harkokin yau da kullum, tare da dan uwansa, Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Mohammed bin Zayed, wanda ake ganin shi ne ke tafiyar da mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel