Dalibai zasu kai shekarar 2023 a gida saboda ba zamu janye daga yajin aiki ba, ASUP
- Shugaban kungiyar malaman makarantun Poly na Najeriya ya ce da alamun babu ranar komawa bakin aiki
- Anderson Ezeibe ya yi gargadin cewa har yanzu gwamnatin tarayya ta ki amsa bukatunsu
- A cewarsa Ezeibe, gwamnatin tarayya ta dade tana nuna cewa ba gaske take ba wajen shawo kan matsalan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Illaro, jihar Ogun - Duk da halin da daliban Najeriya ke ciki na yajin aiki na jami'o'i da kwalejin fasaha, da alamun babu ranar komawarsu makaranta karatu.
Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kungiyar malaman makarantun Poly na Najeriya, Anderson Ezeibe, yace babu alamun za'a janye daga yajin aiki a wannan shekarar ta 2022.
Yayin jawabi a ganawar da mambobin kungiyar suka yi a Kwalejin fasahar tarayya dake Ilaro, jihar Ogun, Ezeibe ya yi gargadin cewa gwamnatin tarayya har yanzu bata biya musu bukatunsu ba, duk da yarjejeniyar da sukayi shekara daya yanzu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A riwayar Punch, Ezeibe ya ce yajin aikin gargadi na makonni biyu da suka shiga kwanan nan suna yi ne don nunawa gwamnati bacin ransu.
A cewarsa:
"A Najeriya kadai zaku shiga yajin aiki don a yi yarjejeniya, sannan ku sake shiga wani yajin aiki don a aiwatar da yarjejeniyar."
"Muna kira ga gwamnatin Najeriya da jama'a su shaida irin rainin hankalin da hukumomin gwamnati ke yi. "
"Kuma mambobinmu su shirya shiga yajin aiki na gaske, wannan na mako biyu ne kadai, hakan na nufin zamu sake shiga wani idan gwamnati bata tashi tsaye ba."
Legit Hausa ta tuntubi wani dalibi mai karatu kwalejin fasaha ta jihar Kaduna watau Kadpoly, AbdulRaqib Ishaq, kan halin da dalibai suka shiga kan wannan jawabi.
Ya bayyanawa wakilin Legit cewa wannan yajin aiki ba karamin illa bane ga ilmin dalibai, tattalin arziki da kuma harkar tsaro.
Yace:
"Wannan abu zai lalata manhajar karatun dalibai, kudin shigan da makarantu ke samu zai tsaya kuma da yiwuwan dalibai su shiga harkar banza saboda zaman kashe wando."
Muddin ba'a yi sulhu da ASUU ba, ba zamu bari ayi zabe ba: Daliban Jami'a
Daliban jami'ar Obafemi Awolowo University (OAU), Ile-Ife, jihar Osun sun cigaba da zanga-zanga bisa yajin aikin ASUU dake gudana.
Daliban sun lashi takobin cewa ba zasu bari ayi zabe ba muddin ba'a bude musu makarantu sun koma aji ba, rahoton Vanguard.
Daliban sun taru gaban kofar makarantar misalin karfe 7 na safe da littafan rubutu inda sukayi ikirarin ko anan Malamansu su zo suyi musu karatu.
Hakazalika suka tare babban titin Ife-Ibadan misalin karfe 10 na safe wanda hakan yayi sanadiyar cinkoson motoci.
Asali: Legit.ng