Yanzu-Yanzu: FG Ta Yi Garambawul a Tuhumar Nnamdi Kanu, Ta Lissafa Lauyoyinsa Cikin Wadanda Ake Tuhuma

Yanzu-Yanzu: FG Ta Yi Garambawul a Tuhumar Nnamdi Kanu, Ta Lissafa Lauyoyinsa Cikin Wadanda Ake Tuhuma

  • Za a sake gurfanar da shugaban haramtaciyyar kungiyar yan aware masu neman kafa Biafra, Nnamdi Kanu kan wasu sabbin tuhume-tuhume shida
  • Hakan ya biyo bayan Mai Sharia Binta Nyako ta zaka rana na sauraron neman beli da Nnamdi Kanu ya shigar
  • A yanzu, Gwamnatin Tarayyar Najeriya, FG, ta yi ikirarin cewa lauyoyin Kanu suma ana tuhumarsu da laifi domin sun cigaba da tattaunawa da shi bayan ya tsere

Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta sake gurfanar da tsararren shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, kan sabbin tuhume-tuhume shida masu alaka da cin amanar kasa, rahoton Vanguard.

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan Mai Shari'a Binta Nyako ta tsayar da rana domin sauraron bukatar da Kanu ya shigar na neman a bada shi beli.

Yanzu-Yanzu: FG Ta Yi Garambawul a Tuhumar Nnamdi Kanu, Ta Lissafa Lauyoyinsa Cikin Wadanda Ake Tuhuma
FG Ta Yi Garambawul a Tuhumar Nnamdi Kanu, Ta Lissafa Lauyoyinsa Cikin Wadanda Ake Tuhuma. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Wani cikin tawagar lauyoyin Kanu, wanda ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa a ranar Laraba, FG ta yi kwaskwarima a tuhume-tuhumen da ta ke yi wa Kanu, inda ta lissafa lauyoyinsa Ifeanyi Ejiofor da Maxwell Opara, a matsayin wadanda ake tuhuma, The Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tserewa zai yi: Yadda aka kaya a kotu kan batun belin shugaban 'yan IPOB Nnamdi Kanu

Matsayar Gwamnatin Tarayya

An tattaro cewa gwamnatin tarayyar, ta yi zargin cewa lauyoyin, sun kasance suna tuntubar Kanu bayan ya tsere daga kasar a yayin da aka bada shi beli.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan za a iya tuna wa an sake kama Kanu ne aka dawo da shi Najeriya daga Kenya, a wani yanayi da ya janyo cece-kuce.

Kotun, a watan Afrilu ta yi watsi da takwas cikin tuhume-tuhume 15 masu alaka da cin amanar kasa da FG ke yi wa Kanu.

Alkaliya, Mai Sharia Binta Nyako, a ranar 8 ga watan Afrilu ta yi watsi da takwas cikin tuhume-tuhume 15 na cin amanar kasa da FG ke yi wa Kanu.

Mai Sharia Nyako ta ce tuhume-tuhumen maimaici ne kuma an gaza gabatar da sahihin hujjar da ke tabbatar an aikata su a kotun.

Kara karanta wannan

Taron siyasa a Plateau: Atiku ya ba da hakuri bisa fatattakar 'yan jarida da ya yi

Ku dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164