Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 sun kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30

Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 sun kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30

  • Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama hanya mafi hadari a fadin Najeriya a shekarun baya-bayan nan
  • Bayan garkuwa da mutane da ake yi da matafiya, har yanzu ba'a daina haduran mota dake hallaka rayukan mutane ba
  • Gwamnatin tarayya tace ranar Litinin jirgin kasan Abuja-Kaduna zai dawo jigilar mutane

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Mumunar hadari a kauyen Katari, hanyar Abuja zuwa Kaduna, ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 20 da sanyin safiyar ranar Talata, 18 ga watan Mayu, 2022.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wata motar haya ta shige cikin wata mota tirelan dake ajiye a bakin titi.

Wani idon shaida ya bayyana cewa dukkan wadanda ke cikin motan suka kone kurmus yayinda direban tirelan ya gudu.

Majiyar ta ce hadarin ya faru ne misalin karfe 5 na asuba a kauyen Katari.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Sakta kwamandan hukumar kiyaye haduran FRSC, Hafiz Mohammed, ya tabbatar da cewa dukkan wadanda ke cikin motar suka kone kurmus.

Hanyar Abuja-Kaduna
Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30 Hoto: @leadership
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan bindiga sun sake kai hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da matafiya da dama a kan sananniyar hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Talata.

Wani shaidan gani da iso ya faɗa wa BBC hausa cewa maharan sun aikata ta'asar ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar a kauyen Katari da ke kan hanyar.

A cewarsa sai bayan maharan sun gama cin karensu ba babbaka, sannan jami'an tsaro masu yawa suka dira wurin domin kawo ɗauki.

Wata majiya daga Katari ta ce tun da safiyar Talata, maharan suka farmaki garin suka sace mutum 16, da yamma kuma misalin karfe 4:00 da motsi suka toshe hanya.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Titin Abuja-Kaduna: El-Rufa'i ya bada shawarar tayar da wasu garuruwa uku dake kan hanyar

Gwamnan jihar Kaduna,Nasir El-Rufai, a ranar Alhamis ya bada shawaran tayar da kauyukan Katari, Rijana da Akilibu, dake kan titin babbar hanyar Kaduna-Abuja.

Yace masu kaiwa yan bindiga bayanai ne suka cika wadannan kauyuka.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne yayin karban rahoton irin hare-haren yan bindigan da jihar Kaduna ta fuskanta tsakanin watar Junairu da Maris, rahoton TheNation.

Ya ce yanzu yan ta'adda sun tashi daga Arewa maso gabas, sun shiga Arewa maso yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng