Ba zamu kara farashin wutan lantarki ba, Hukumar NERC ta bayyana

Ba zamu kara farashin wutan lantarki ba, Hukumar NERC ta bayyana

  • Karo na biyu, gwamnatin tarayya ta jaddada cewa ba zata kara farashin wutan lantarki ba a shekarar nan
  • Hukumar NERC ta tabbatar da lamarin nazari da bitan kamfanonin wuta da aka saba kowace shekara
  • Najeriya, har ila yau, na fama da matsalar rashin tsayayye da ingantaccen wutan lantarki

Abuja - Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC ta yi fashin baki kan zaman sake duba harkar wuta da ta jagoranta, inda tace hakan ba ya nufin za'a kara farashi.

Hukumar ta bayyana hakan ne a jawabin da ta fitar ranar Talata kan bitan wata shida-shida da aka saba kan kamfanonin da aka ba lasisi, rahoton Punch.

A cewar NERC, an yi fashin bakin ne bisa jita-jitan dake yawo cewa kamfanonin rarraba wuta sun kara farashin lantarki.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Hukumar ta sanar da cewa bisa dokar sashen wuta Electric Power Sector Reform Act, EPSRA, zata fara zaman nazarin MYTO na 2022 a watan Yuli.

Hukumar tace za'ayi nazari da bitan ne don ganin irin sauye-sauyen da aka samu wajen samar da wutan lantarki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar NERC ta bayyana
Ba zamu kara farashin wutan lantarki ba, Hukumar NERC ta bayyana Hoto: NERC
Asali: Facebook

Rashin wutan lantarki a Najeriya

Legit Hausa ta samu tattaunawa da wasu yan Najeriya bisa matsalar rashin tsayayye da ingantaccen wutan lantarki a kasar.

A hirar wakilin Legit da Malam Muddasir mazaunin garin Abuja, ya bayyana cewa tsawon kwanaki biyu kenan babu lantarki a mafi akasarin unguwannin birnin tarayya.

A cewarsa, abin ya yi tsanani saboda ko man feturin siya don zubawa a janareto babu.

Yace:

"Rabonmu da wutan lantarki tun ranar Lahadi, gashi kuma gidajen mai basu sayarwa mutane mai a jarka, dole sai mutum ya gingimi janareta cikin mota."

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Bamu bada izinin kara farashin wutan lantarki ba tukun, Hukumar NERC

Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC ta bayyana cewa bata bada izinin kara farashin wuta ba tukunna.

Shugaban hukumar, Garba Sanusi, yayin hira da manema labarai ranar Juma'a ya karyata rahotannin da ke kafafen yada labarai cewa za'a yi karin farashi.

Yace duk wanda ya ga an kara masa kudin wuta ya shigar da kara da hujja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel