Yanzu-Yanzu: EFCC Ta Kama Tsohuwar Kakakin Majalisa, Patricia Etteh, Kan Zargin Almundaha

Yanzu-Yanzu: EFCC Ta Kama Tsohuwar Kakakin Majalisa, Patricia Etteh, Kan Zargin Almundaha

  • Jami'an EFCC sun kama tsohuwar shugaba majalisar wakilan tarayyar Najeriya, Mrs Patricia Etteh a birnin tarayya Abuja
  • An kama Mrs Etteh ne bisa zarginta da karbar Naira Miliyan 130 daga hannun wani dan kwangila hukumar NDDC ta bawa aikin lantarki
  • Bayanai sun nuna cewa Etteh ba direkta bace a kamfanin da NDDC ta bawa kwangilar kuma bata da hannun jari don haka abin tambaya ne

FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta kama tsohuwar kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Patricia Etteh, kan zargin damfara da ya shafi hukumar cigaban yankin Neja Delta, NDDC, rahoton Channels.

Hukumar yaki da rashawar ta kama Etteh ne a ranar Talata a birnin tarayya a Abuja domin yi mata tambayoyi.

Yanzu-Yanzu: EFCC Ta Kama Tsohuwar Kakakin Majalisa, Patricia Etteh, Kan Zargin Almundaha
EFCC Ta Kama Tsohuwar Kakakin Majalisa, Patricia Etteh, Kan Zargin Almundaha. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Facebook

Daliln da yasa aka kama Etteh don yi mata tambayoyi

Kara karanta wannan

Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun kashe 3 a dangin shugaban karamar hukuma da mai gadi

A lokacin hada wannan rahoton, ana yi wa tsohuwar yar majalisar tambayoyi ne kan zarginta da karbar Naira Miliyan 130 daga hannun wani dan kwangila daga Hukumar Cigaban Yankin Neja Delta, NDDC, na aikin samar da lantarki daga hasken rana a Jihar Akwa Ibom.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An bada kwangilar aikin ne da kamfani mai suna Phin Jin Project Limited a 2011 kan kudi Naira Miliyan 240. Ba'a tabbatar ko kamfanin na da rajista da CAC ba.

Daya daga cikin masu binciken ya ce watanni bayan an biya dan kwangilar kudin fara aiki, an tura wa Mrs Etteh Naira Miliyan 130 daga kudin kuma ita ba direkta bace ko mai hannun jari a kamfanin a iya bayanai da aka sani yanzu.

Ya ce:

"Kudin da aka biya ta yana da yawa kuma abin zargi ne. Tana ikirarin cewa dan kwangilar biyan bashi ya yi mata amma muna tantama kan hakan. Don haka ana bincika ikirarin ta.

Kara karanta wannan

Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 sun kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30

"Duk da cewa kudin da aka biya ya fi na kwangilar. A maimakon N240m, an biya N287m. Wannan abin daure kai ne kuma ya kamata dan kwangilar ya yi bayani shi yasa aka gayyace ta ana mata tambayoyi."

An zabi Etteh ne a matsayin kakakin majalisa a shekarar 2007 amma ta yi murabus watanni kadan bayan zargin bannatar da kudi.

Ita kadai ce mata a tarihin Najeriya da aka taba zaba kakakin majalisar tarayya.

An Kama Akanta-Janar Na Tarayyar Najeriya, Ahmed Idris

A wani rahoton, Jaridar Premium Times ta ce ta samu sahihin rahoto da ke tabbatar da cewa an kama Akanta Janar na tarayyar Najeriya, Ahmed Idris, kan zargin almundahanar kudi da karkatar da kudin gwamnati.

Wadanda suke da masaniya kan lamarin sun ce jami'an EFCC na Kano ne suka kama Idris a yammacin ranar Litinin kuma za a tafi da shi Abuja domin amsa tambayoyi.

Majiyoyi sun ce EFCC ta dade tana bincike a kan zargin karkatar da Naira biliyan 80 na kudin gwamnati ta hanyar wasu kwangiloli na bogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164