Matasa sun nuna fushinsu yayin da wata Naomi Goni ta kara ɓatanci ga Annabi SAW, an kama 3
- Mutane sun fito zanga-zanga har sansanin sojojin Division 7 inda suka nemi a fito musu da Naomi Goni da ake zargin ta yi batanci ga Annabi
- Hukumar yan sanda ta jihar Borno ta bayyana cewa jami'anta sun kama mutum uku ɗauke da wasu abubuwan cutarwa cikin masu zanga-zanga
- Kwamishinan yan sanda, Abdu Umar, ya ce ba ya tsammanin sun aikata wani laifi amma sai an gama bincike
Borno - Hukumar yan sanda reshen jihar Borno ta kama mutum uku yayin da matasa suka nuna fushinsu kan wasu kalaman ɓatanci da wata Naomi Goni ta yi wa Annabi Muhammada SAW a shafin Facebook.
Daily Trust ta rahoto cewa ana zargin Naomi da yin wasu kalamai da ba su dace ba lokacin da take martani kan kashe Deborah Samuel, dalibar kwalejin Shehu Shagari, wacce ta zagi fiyayyen halitta.
Kwamishinan yan sanda na Borno, CP Abdu Umar, shi ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai inda ya yi bayani kan halin da ake ciki a birnin Maiduguri.
Ya ce mutum uku da aka kama kuma ake zargi sun shiga hannu ne bayan ganin su ɗauke da Man Fetur a cikin jarkoki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Umar ya gargaɗi mazauna jihar da su guji yin amfani da wannan zanga-zangar wajen ta da zaune tsaye a jihar Borno.
Kwamishinan ya ce:
"A halin yanzu waɗan da ake zargi suna tsare a hannun mu, bana tunanin suna da alaƙa da aikata wani laifi amma har sai an gama bincike."
CP Ya ce duk wani taro da ya saɓa wa doka haramun ne yin shi a jihar, inda ya ƙara da cewa, "Jami'an tsaro na cigaba da yawon sintiri a cikin birni domin tarwatsa taron da ya saɓa wa doka."
Sokoto: Mutane sun mamaye tituna da zanga-zanga, sun nemi a saki waɗan da suka kashe ɗalibar da ta zagi Annabi
Yadda matasa suka nuna fushin su kan Batanci ga Annabi SAW
Tun da farko Ɗaruruwan mutane suka mamaye sasanin sojin 7 Division Garrison a cikin garin Maiduguri don nuna fushin su kan kalaman ɓatanci da Goni ta yi.
Masu zanga-zangan sun rika ƙona tayoyi a kofar shiga wurin kuma suka toshe hanyar Bypass kasancewa a nan ne Naomi Goni ke zaune tare da wani Soja, suka bukaci a fito da ita.
A wani labarin kuma Gwamnan Nasarawa ya yi Allah wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi, ya roki CAN ta yi hakuri
Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya roki kungiyar CAN ta yi hakuri kada ta fara zanga-zangar da ta shirya kan kashe Deborah a Sokoto.
Gwamnan wanda ya yi Allah wadai da kisan ɗalibar wacce ta zagi Annabi, ya ce gwamnati zata ɗau mataki kan mutanen da suka yi kisan.
Asali: Legit.ng