Gwamnan Nasarawa ya yi Allah wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi, ya roki CAN ta yi hakuri

Gwamnan Nasarawa ya yi Allah wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi, ya roki CAN ta yi hakuri

  • Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya roki kungiyar CAN ta yi hakuri kada ta fara zanga-zangar da ta shirya kan kashe Deborah a Sokoto
  • Gwamnan wanda ya yi Allah wadai da kisan ɗalibar wacce ta zagi Annabi, ya ce gwamnati zata ɗau mataki kan mutanen da suka yi kisan
  • Ya ce gwamnatinsa ta ɗauki kwararan matakai da zasu hana irin haka ta faru a jihar Nasarawa

Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi Allah wadai da kisan Deborah Samuel, dalibar aji biyu a kwalejin Shehu Shagari da ke Sokoto, ya kira lamarin da rashin tausayi.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a jawabinsa na buɗe taro a wurin taron tsaro na gaggawa da ya kira a gidan gwamnati da ke Lafiya, ranar Litinin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kisan Deborah: Kungiya ta nemi a kamo limamin BUK bisa zargin halasta jinin Bishop Kukah

Gwamna Sule na jihar Nasarawa.
Gwamnan Nasarawa ya yi Allah wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi, ya roki CAN ta yi hakuri Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sule ya roki ƙungiyar kiristoci CAN reshen jihar ta yi hakuri kar ta shiga zanga-zangar da uwar ƙungiyar ta ƙasa ta shirya, a cewarsa gwamnatin tarayya da ta Sokoto na kokarin shawo kan lamarin.

Daily Trust ta rahoto Gwamna Sule ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kamar yadda kuka sani, shugaban ƙasa ya yi Allah wadai da kisan, majalisar tarayya, Sarkin Musulmi, kungiyar CAN, kungiyar gwamnonin arewa duk sun haɗu sun yi Allah wadai."
"Kuma waɗan da ake zargin suna da hannu a kashe ta sun shiga hannu, zamu bi kadin lamarin har ƙarshe. Abun takaici ne da rashin sa'a hanyar da aka bi aka kashe ɗalibar."

Meyasa ya kira taron tsaro?

Gwamnan ya ce daga cikin maƙasudin kiran taron shi ne don yi wa iyayen Deborah ta'aziyya, kiristoci da ma mutane baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Sokoto: Wani Malami ya yi alkawarin daukar nauyin iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi, yace sun gama wahala a duniya

Ya kuma yi kira ga CAN a Nasarawa ka da ta shiga zanga-zangar da suka shirya saboda hatsarin da hakan da tsoron wasu bara gurbi ka iya shiga su canza lamarin zuwa tashin hankali.

Gwamna Sule ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakan kare rayukan al'umma da kuma tabbatar da irin haka ba ta faru ba a jiharsa ta Nasarawa.

A wani labarin kuma Jami'an tsaro sun ɗauki mataki bayan wata Kirista ta sake kalaman Batanci ga Annabi a Borno

Yayin da aka fara jitar-jitar wata kirista ta sake kalaman batanci ga Annabi, Jami'an tsaro sun shirya ba da tsaro a birnin Maiduguri.

Rahoto ya nuna cewa wacce ake zargi da yin ɓatancin ta taɓa zama a jihar Borno, amma ta jima da barin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262