Karamin dalili: Saurayi ya fasa auren budurwa saboda ta ki shan ruwa a gidansu

Karamin dalili: Saurayi ya fasa auren budurwa saboda ta ki shan ruwa a gidansu

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta ba da labarin yadda tsohon saurayinta ya rabu da ita bayan wani abin mamaki da ya faru a gidansa
  • A cewar budurwar a shafin sada zumunta na Facebook mai suna Chidimma Blessing, ta ziyarci sabon gidan saurayin nata da ke Asaba, inda ya ba ta kofin ruwa ta sha
  • Chidimma ta ce ta ki sha ruwan, ta nace cewa ba ta jin kishirwa, lamarin da bai yi wa masoyinta dadi ba, wanda ya ce ba daidai banne ta ki amincewa da tayin nasa

Najeriya - Rahoto ya bayyana cewa wani dan Najeriya ya rabu da budurwarsa bayan ta ki shan ruwan a kofin da da ya debo ya bata.

A cewar budurwar mai suna Chidimma Blessing wadda ta bada labarin ta a shafinta na sada zumunta na Facebook, ta ziyarci saurayin nata ne, inda ya garzaya zuwa madafa ya kawo mata ruwa. Amma ta hakikance kikam ta ki shan ruwan.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Yadda saurayi ya fasa auren budurwarsa saboda kin shan ruwa a gidansu
Raina kama: Saurayi ya fasa auren budurwa saboda ya bata ruwa ta ki sha | Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Shiyasa ban sha ruwan ba

A cewar Chidimma, ta ki shan ruwan ne saboda ba ta jin kishirwa, amma saurayin nata a lokacin ya zargi wani abu daban, inda ya ce ba daidai bane ta ki shan ruwa a gidansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta rubuta a Facebook cewa:

"Da zarar isanmu gidansa, da sauri ya shiga madafa ya miko min ruwa, na ce masa ba kishirwa nake ji ba, ya amsa da cewa kada in ki duk wani abu da zai bani amma na nace bana jin kishirwa.
“Yayarsa ta yi kururuwa tun daga bangarenta cewa ba daidai bane naki shan ruwa a wurinsu amma duk da haka nace ba kishirwa nake ji ba, a fusace ya mayar da ruwan, yanayinsa a kaina ya canza, bayan mun bar gidansa ya daina kira na, idan na kira shi ba ya dauka.

Kara karanta wannan

Na Gaji: Matata Tana Yawan Lakaɗa Min Duka, Maigidanci Ya Roƙi Kotu Ta Raba Aurensu

"Haka suka susuta batun auren saboda kawai ban sha ruwan da suka bani ba."

'Yan Facebook sun tofa albarkacin bakinsu

Amaka Micheal ta ce:

"Hmmm bin sa zuwa Asaba kadai ma kin yi babbar kasada. Haka nan da kika ki shan ruwa, hmmm duk da kin yi gaskiya amma da a lokacin baki isa gida ba fa? Ki yi tunani sosai."

Mma JT tace:

"Me yasa kIka bishi har Asaba? Kuma gidanshi idan yayi miki wani mummunan abu fa? Batu ne na yaudara kawai. Ya yi kyau da kika bi son zuciyarki kada kiji haushi don ya daina kira. Saboda yana jin kina tunanin zai saka miki guba ne, don haka abin da ya yi ba laifi ba ne."

Soyayyar Facebook: Mata ƴar Indiya ta fasa auren masoyinta ɗan Najeriya a gaban mutane ranar ɗaurin aure

A bangare guda, wani mutum dan Najeriya ya shiga cikin damuwa bayan matar da zai aura ta yi watsi da shi a yayin da ake daf da daura musu aure, LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Daliban Najeriya sun gano mafita, za su tara wa lakcarori kudi kawai

Lamarin ya faru ne a binrin Bangladesh kuma an gano cewa matan da mijin sun hadu ne a shafin dandalin sada zumunta na Facebook.

Daga bisani ne matar ta gayyaci saurayin dan Najeriya zuwa kasarta wato Indiya domin a daura musu aure.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel