Yanzu-yanzu: Fursunoni sun gudu sakamakon ruwan saman da ya rusa katanga a jihar Delta

Yanzu-yanzu: Fursunoni sun gudu sakamakon ruwan saman da ya rusa katanga a jihar Delta

  • Ruwan saman da a akayi ya yi sakamakon rushewar katangar gidan yari a jihar Delta ranar Talata
  • Fursunoni masu laifi da aka tsare a cikin gidan yarin sun gudu, amma hukumar gidan tace babu wanda ya gudu
  • An tura dimbin jami'an yan sanda da soji don hana wadanda ke tsare ciki kokarin afkawa ma'aikatan kurkukun

Delta - Akalla fursunoni uku sun gudu daga gidan yarin Agbor dake jihar Delta yayinda katanga ya rushe sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwaryar da aka yi ranar Talata.

Premium Times ta ruwaito cewa fursunonin sun arce ne bayan ganin rushewar katangar dake Arewacin gidan yarin.

Tuni dai an tura jami'an ganduroba, yan sanda da sojoji gidan yarin don gudun kada sauran dake ciki suyi kokarin guduwa.

Hotunan katangar da ta fadi sun bayyana inda jami'an gidan yari ke tsaye kan katangar da ta rushe.

Kara karanta wannan

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

An tattaro cewa rushewar katangar na baiwa jami'an gidan yarin tsoro saboda ana iya kai musu hari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fursunoni
Yanzu-yanzu: Fursunoni sun gudu sakamakon ruwan saman da ya rusa katanga a jihar Delta Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Premium Times ta kara da cewa Kakakin hukumar gidajen yarin Najeriya, Francis Enabore, ya tabbatar da labarin rushewar katangar. Amma ya karyata rahoton cewa fursunoni sun gudu.

A cewarsa:

"Lallai hakan ya faru. Abinda ya faru shine wani sashen katangar ya fadi sakamakon ruwan sama mai karfi. Dukkan fursunonin na nan babu wanda ya gudu, babu wanda ya ji rauni."
"Ban dade da na gama magana da jami'an gidan yarin ba kuma sun tabbatar min komai na nan lafiya."

Afuwar da Shugaba Buhari ya yi wa tsofaffin barayin kasa ta jawo an maka shi gaban kotu

Kungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project wanda aka fi sani da SERAP ta shigar da kara a kotu a kan Mai girma Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da wasu 20 a Kaduna

Jaridar Punch a wani rahoto da ta fitar a ranar Lahadi, 9 ga watan Mayu 2022, ta ce SERAP ta na kalubalantar afuwar da shugaban Najeriyan ya yi wa masu laifi.

Mataimakin Darektan wannan kungiya mai zaman kan ta, Kolawole Oluwadare ya fitar da wani jawabi na musamman, inda ya bayyana matsayar da suka dauka.

Mista Kolawole Oluwadare ya ce sun kai shugaban kasa kotu ne saboda yafewa Sanata Joshua Dariye da Jolly Nyame laifin da suka aikata na satar kudin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng