Da dumi-dumi: Daliban kwalejin ilimin Shehu Shagari sun kashe daliba kan zargin batanci ga Annabi

Da dumi-dumi: Daliban kwalejin ilimin Shehu Shagari sun kashe daliba kan zargin batanci ga Annabi

  • Wasu dalibai a jihar Sokoto sun afkawa wata daliba mai suna Deborah da aka yiwa zargin tayi kalaman batanci
  • Jami'an yan sanda sun yi kokarin ceton dalibar amma daliiban suka kwaceta hannunsu kuma suka hallaka
  • Daliban sun tuhumeta da yin kalaman batancin a shafin manhajar Whatsapp na yan ajinsu

Sokoto - An kashe wata dalibar kwaljin ilmin Shehu Shagari dake jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi)

21st CENTURY CHRONICLE ta ruwaito cewa an kashe dalibar mai suna Deborah bayan an bukaci ta janye kalamanta amma taki.

Rahoton ya kara da cewa wannan abu ya faru ne ranar Alhamis da safe.

Yanzu dai gwamnatin jihar Sokoto ta rufe makarantar, riwayar TVCNews.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Gwamnatin Sokoto ta dakatar da komawa makarantu, ta kara mako guda

Bidiyoyi a kafafen sada zumunta sun nuna yadda dalibai suka yiwa dalibar.

kwalejin ilimin Shehu Shagari
Da dumi-dumi: Daliban kwalejin ilimin Shehu Shagari sun kashe daliba kan zargin batanci ga Annabi Hoto: tvcnewsng
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa Deborah ta furta kalaman batancin ne a dakin kwanan dalibai sakamakon rashin jituwan da ya auku tsakaninta da wasu dalibai.

Daya daga cikin daliban da ta bukaci a sakaye sunanta tace:

"An bukaceta ta janye kalamanta amma ta 'kiya, hakan ya fusata sauran dalibai Musulmai a kwalejin."

Wata majiya ta bayyana cewa jami'an tsaron makarantar sun boyeta a ofishinsu amma fusatattun matasa suka fi karfinsu, suka kasheta, sannan suka kona gawarta.

Ance jami'an tsaro yanzu sun mamaye makarantar.

Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari

A wani abarin kuwa, kotu ta yanke hukunci kan karar da aka shigar kan Shahararren matashin da ke ikirarin bai yarda da Allah ba, dan asalin jihar Kano, Mubarak Bala, ranar Talata, 5 ga Afrilu, 2022.

Kara karanta wannan

A zauna lafiya: Gamayyar gwamnonin Arewa sun yi Alla-wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi

Wata babban kotun jihar Kano dake zamanta a Audu Bako Secretariat ta yanke masa hukuncin daurin shekaru ashirin da hudu a gidan gyaran hali bayan amsa laifukan da ake tuhumarsa da su.

Gabanin yanke masa hukunci, Mubarak ya bukaci kotu ta sassauta masa saboda bai aikata abubuwan da ake zarginsa da su ba don tada tarzoma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: