2023: Zan nunka rokon Allah don ka samu nasara, Ɗahiru Bauchi ga Osinbajo
- Fitaccen Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya nuna goyon bayansa ga Yemi Osinbajo a zaɓen 2023
- Malamin ya ce ya jima ya na wa mataimakin shugaban Addu'a don haka zai nunka rokon Allah ya samu nasara a zaɓe
- A ranar Talata, Osinbajo ya kai ziyara jihar Bauchi a wani bangare da neman shawarin masu ruwa da tsaki
Bauchi - Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ranar Laraba ya ce ya jima yana rokon Allah ya ba mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, nasara a zaben shugaban ƙasa.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Shehin Malamin ya yi alƙawarin kara nunka addu'ar da yake wa Osinbajo.
A ranar Talata, Osinbajo, ya kai ziyara jihar Bauchi a wani ɓangaren yawon neman shawari wurin masu ruwa da tsaki da zawarcin Deleget game da burinsa a 2023.
'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya
Sheikh Bauchi ya bayyana gamsuwarsa kan Osinbajo ya ɗora daga inda shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai aje, inda ya ƙara da alƙawarin nunka rokon Allah don nasarar Osinbajo.
Malamin addinin Musuluncin ya ce:
"Zan jima ban mance wannan ziyarar ba saboda daga ƙarshe mun haɗu bayan tattaunawa a waya. Na jima ina maka addu'a kafin yanzu da kake takara, zan nunka addu'ar da nake maka."
"Duk abinda ka sa a zuciyarka Allah zai baka, zamu goya maka baya domin nan gaba idan ka zo mana ziyara zai kasance kana matsayin shugaban ƙasar nan."
Osinbajo ya yaba wa Ɗahiru Bauchi
Tun da farko, Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ya gode wa Malamin bisa kyakkyawar tarban da aka masa hannu biyu kuma ya yaba masa kan rawar da yake taka wa wajen dunƙulewar Najeriya.
PM News ta rahoto Osinbajo ya ce:
"Na yi farin cikin ganin ka, saboda ka kasance ɗaya daga cikin ginshikai masu karfi na haɗin kan kasar nan da kuma hakuri game da harkokin Addini."
"Kai wani mutum ne da yake yawan magana kan zaman lafiya kuma ko da yaushe kana ƙara mana zumma. Ina sauraron karatunka a lokuta da dama wajibi na yaba maka."
A wani labarin kuma Daruruwan mambobin APC, PDP sun bi su Kwankwaso, sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP a Kaduna
Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta ƙara karfi a jihar Kaduna yayin da take shirin tunkarar babban zaɓen 2023 da ke tafe.
Mambobin manyan jam'iyyu APC da PDP mutum 1,000 sun sauya sheka zuwa NNPP a wani yankin jihar ta Kaduna.
Asali: Legit.ng