Wani mutum ya mutu yayinda yake kokarin birne matar da ya kashe cikin gidansa

Wani mutum ya mutu yayinda yake kokarin birne matar da ya kashe cikin gidansa

  • Wani mutumi ya mutu yayinda yake bizne matar da ya kashe cikin gidansa a birnin South Carolina
  • An gudanar da binciken Autopsy kuma an gano ainihin abinda ya auku tsakaninsu, yan sanda suka bayyana
  • Hukumomi sun bayyana cewa mutumin ya kashe matar da hannunsa sannan ya mutu yayinda yake birneta

Amurka - Wani mutumi ya mutu sakamakon bugun zuciya yayinda yake kokarin birne wata mata da ya shake har lahira a bayan gidansa, jami'ai a jihar South Carolina, Amurka suka bayyana.

Shugaban yan sanda yankin Edgefield, Jody Rowland, da shugaban hukumar ajiye gawawwaki, David Burnett, a jawabin da suka saki ranar Talata sun tabbatar da hakan, WJBF.com ta bayyana.

A cewarsu, an tura jami'ai wani gida a layin Tanglewood Drive, Trenton, South Carolina, ranar 7 ga Mayu bayan samun rahoton ganin gawar wani mutumi cikin gidansa.

Kara karanta wannan

Lauya ya kwashe kudin dake akawunt din dan sanda bayan ya mutu, EFCC ta damkeshi

Yayinda suka isa gidan, sun tsinci gawar Joseph McKinnon, dan shekara 60 a kasa, kuma daga baya suka ga wata gawa nade cikin leda a sabon ramin da aka tona, Jawabin ya kara.

Daga baya an gano gawar wata mata ce mai sune Patricia Dent, wacce ke zama tare da McKinnon a gidan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mutum ya mutu yayinda yake kokarin birne matar da ya kashe cikin gidansa
Wani mutum ya mutu yayinda yake kokarin birne matar da ya kashe cikin gidansa
Asali: UGC

Sakamakon Binciken gawa (autopsy) da aka fitar ranar Litnin ya nuna cewa McKinnon ya yi mutuwar ajali amma matar kasheta akayi ta hanyar makure mata wuya, cewar jawabin.

Wani sashen jawabin yace:

"Hujjojin da aka tattara a wajen, da kuma jawabin masu idanuwa shaida sun taimakawa masu bincike wajen gano McKinnon ya kashe Madam Dent cikin gidan."
"Bayan kasheta, Mr. McKinnon, ya nadeta cikin leda kafin jefata cikin kabarin da ya haka. Ya fara rufeta da kasa sai zuciyarsa ta buga kuma ya mutu."

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

A Bauchi, wani mutum ya yi garkuwa da diyar makwabcinsa kuma ya kasheta bayan karban kudin fansa

A nan gida kuwa, Jami'an tsaro sun damke wani mutumi mai suna Kabiru Abdullahi wanda ake zargi da kisan diyar makwabcinsa, Khadija yar shekara biyar a jihar Bauchi.

Kakakin hukumar Civil Defence na jihar, Garkuwa Adamu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Litinin, rahoton ChannelsTV.

Ya yi bayanin cewa an damke Abdullahi ne tare da Alhaji Yawale kan zargin garkuwa da diyar Abdullahi Yusuf a Sabon Gari Narabi a karamar hukumar Toro.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel