Pantami Zai Jagoranci Taron Duniya Na Ƙungiyar Sadarwa Ta Shekarar 2022
- Kungiyar Sadarwa ta Kasa da Kasa, ITU, ta zabi Isa Pantami, Ministan sadarwar Najeriya, a matsayin shugaban Taron Kungiyar Bayanai ta Duniya (WSIS) na 2022
- Za a yi taron ne a hedkwatar Kungiyar sadarwa ta kasa da kasa da ke Geneva cikin Kasar Switzerland kamar yadda hadimin ministan na harkar bincike da ci gaba, Dr Femi Adeluyi ya bayyana a wata takarda
- Ya ce an bayyana wa ministan wannan nadin ne ta wata wasika wacce Sakatare Janar na ITU, Houlin Zhao ya aiko masa kuma hakan ya biyo bayan dagewarsa da iliminsa a bangaren sadarwa
Ministan Sadarwa, Isa Pantami zai jagoranci taron Kungiyar Bayanai ta Duniya ta shekarar 2022 bisa nadin da Kungiyar Sadarwa ta Kasa da kasa (WSIS) ta 2022 ta yi masa, TVC News ta ruwaito.
Za a yi taron ne a hedkwatar Kungiyar Sadarwar ta Kasa da Kasa da ke Geneva cikin Switzerland.
Kamar yadda takardar da hadimin ministan na bangaren bincike da ci gaba, Dr Femi Aduluyi ya saki ta nuna, an sanar da ministan batun nadin na shi ne ta wata takarda wacce babban sakataren ITU, Houlin Zhao ya aika masa.
Nadin Pantami ya biyo bayan ganin jajircewarsa akan ci gaba a harkar sadarwa
An nada Pantami ne saboda jajircewarsa a hanyar bayanai da ilimin fannoni da kuma dagewarsa akan harkokin WSIS, kamar yadda Zhao ya shaida. Kuma sai da su ka yi bincike kwarai kafin su dauki matakin.
TVC News ta ruwaito cewa akwai manyan kusoshin da za su halarci taron ciki har da ministocin kasashen ITU.
Kamar yadda takardar ta nuna:
“Nadin Pantami ya bai wa Najeriya da kuma Nahiyar Afirka wata babbar dama ta taka rawa a bangaren WSIS a shekararta ta 20, wanda an fara taron ne tun 2003 kuma an ci gaba da yi duk shekara.”
Manuniya ta nuna cewa duniya ta lura da ci gaban da Najeriya ta samu a fannin sadarwa
Takardar ta ci gaba da bayyana cewa:
“Alamu sun nuna cewa duniya ta ga yadda bangaren sadarwa ya bunkasa a Najeriya karkashin shugabancin Ministan. Hakan ya sa Pantami ya mika godiyarsa ga Shugaba Muhammadu Buhari akan kwarin gwiwar da ya ke ba shi a bangaren sadarwa.
“Fannin WSIS da hadin gwiwar kungiyoyin UN sun samar da damar bibiyar bayanai da kuma bincike tun shekara 2005. WSIS wacce ITU, UNESCO, UNDP da UNCTAD su ke sarrafawa da hadin gwiwar kungiyoyin majalisar dinkin duniya, ciki har da FAO, ILO, ITC, UNDESA, UNICEF, UNIDO, UNITAR, UNHCR, UNODC, UNEP, UPU, UN Tech Bank, WMO, WIPO, WHO, WFP, Kungiyar matan UN da sauransu.”
Asali: Legit.ng