Kano: Budurwar Abdulmalik Tanko makashin Hanifa Abubakar ta ba da shaida a Kotu

Kano: Budurwar Abdulmalik Tanko makashin Hanifa Abubakar ta ba da shaida a Kotu

  • Budurwar Abdulmalik Tanko da ake zargi da hannu a kisan Hanifa ta bayyana yadda ya yaudare ta da alƙawarin aure da kayan ɗaki
  • Hashim Isiyaku, ɗayan matashin da ake zargin su tare yace Abdulmalik ya yaudaresa da sunan mahaifiyar Hanifa ta sa a yi aikin
  • Bayan sauraron jawaban mutanen biyu. Aƙalin Kotun ya ɗage zaman zuwa 14 ga watan Yuni

Kano - Masoyiyar Abdulmalik Tanko, shugaban makaranta da ake zargi da sace ɗalibarsa har ya kashe ta, Fatima Jibril, ta ce yaudararta ya yi ya sa ta cikin lamarin.

Aminiya Hausa ta rahoto cewa ta shaida wa Kotu cewa Tanko ya mata alƙawarin aure bisa haka ya umarci su sace Hanifa a makarantar Islamiyya.

An gurfanar da Fatima tare da wani Hashim Iyaku a gaban Alkalin babbar Kotun jihar Kano, Mai Shari'a Usman Na'abba, domin kare kan su.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Shari'ar kisan Hanifa Abubakar.
Kano: Budurwar Abdulmalik Tanko makashin Hanifa Abubakar ta ba da shaida a Kotu Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Da suke ba da shaida a gaban Kotun lokuta daban-daban, mutanen biyu sun ce Tanko ya yaudare su har ya kai ga jefa su cikin lamarin garkuwa da ƙaramar yarinyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yar kimanin shekara 25 a Duniya, Fatima ta faɗa wa Kotu cewa Saurayin nata ya ja hankalinta da alƙawarin zai aure ta kuma zai mata kayan ɗaki ya shigar da ita lamarin.

Sai dai budurwar mai siyar da kayan miya, tace tun lokacin da yunkurin sace Hanifa a Islamiyya ya ci tura, ba ta sake ganin Abdulmalik Tanko ba sai lokacin da asirin shi ya tonu aka tafi tare da ita.

Ta ya ya yaudari Hashim Isiyaku?

A nashi bangaren, Hashin Isiyaku, ya ce Tanko ya yaudare shi da cewa wata mata ce ta bukaci su yi garkuwa da ɗiyarta domin hana mijinta ƙarin auren da yake da shirin yi.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da kashe ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto, ya nemi a yi bincike

Hashim ya ce:

"Ya nuna mun hoton a wayarsa, na faɗa masa gaskiya aikin laifi ne amma sai ya shaida mun mahaifiyar yarinyar ce ta nemi haka don haka ba abin da zai faru."
"Da safe ya zo har gida ya ɗauke ni a NAPEP don yin aikin, ya bani lambar wata mace da zamu yi aikin tare ya aje ni a wani wuri. Mun haɗu da Fatima a Kwanar Dakata muka jira fitowar yarinyar daga Islamiyya."
"Bayan tashi daga karatu, yara suka rinka wucewa, mun ga yarinyar amma ɗaukarta a lokacin bai yuwu ba, daga nan sai muka koma gida."

Hashim ya ƙara da cewa bai ƙara sa Abdulmalik a idonsa ba tun ranar sai watarana ya kira shi ya zo don taimaka masa ya binne wani ɓari da matar maƙocinsa ta yi saboda mijin ba ya gari.

Wane mataki Kotu ta ɗauka bayan jin haka?

Alƙalin Kotun, Mai shari'a Usman Na'abba, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga watan Yuni, 2022.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

A wani labarin kuma Hukumar yan sanda ta miƙa cakin Miliyan N60m ga iyalan yan sanda 6 da yan bindiga suka kashe a bakin aiki a Kebbi

Hukumar yan sanda ta jihar Kebbi ta gabatar da cakin zunzurutun kuɗi miliyan N60m ga iyalan yan sanda 6 da suka mutu a bakin aiki.

A ranar 15 ga watan Maris, yan sandan suka rasa rayuwarsu yayin fafatawa da yan bindiga yayin a kamfanin GB Food Company.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262