Da dumi: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya daga kasar Ivory Coast

Da dumi: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya daga kasar Ivory Coast

  • Bayan kwanaki biyu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya daga kasar Ivory Coast
  • Shugaban kasan ya samu rakiyar kimanin ministocinsa guda hudu

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya dira Abuja, birnin tarayya, bayan halartan taron shugabannin kasashen COP15 na majalisar dinkin duniya a Abidjan, kasar Cote'divoire.

Shugaban kasan ya bar Najeriya ne ranar Lahadi, 8 ga Mayu, don halartan taron yaki da fari, da illan da hakan ke da shi kan tattalin arzikin duniya.

A taron, Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi kan kokarin da Najeriya ke yi wajen yaki da fari.

Shugaba Buhari ya samu rakiyan Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan yanayi, Mohammed Abdullahi; ministan noma, Dr Mahmud Mohammed da ministan harkokin ruwa, Suleiman Adamu dss.

Kara karanta wannan

Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

Shugaba Buhari
Da dumi: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya daga kasar Ivory Coast Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng