Da dumi: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya daga kasar Ivory Coast
1 - tsawon mintuna
- Bayan kwanaki biyu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya daga kasar Ivory Coast
- Shugaban kasan ya samu rakiyar kimanin ministocinsa guda hudu
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya dira Abuja, birnin tarayya, bayan halartan taron shugabannin kasashen COP15 na majalisar dinkin duniya a Abidjan, kasar Cote'divoire.
Shugaban kasan ya bar Najeriya ne ranar Lahadi, 8 ga Mayu, don halartan taron yaki da fari, da illan da hakan ke da shi kan tattalin arzikin duniya.
A taron, Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi kan kokarin da Najeriya ke yi wajen yaki da fari.
Shugaba Buhari ya samu rakiyan Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan yanayi, Mohammed Abdullahi; ministan noma, Dr Mahmud Mohammed da ministan harkokin ruwa, Suleiman Adamu dss.
Asali: Legit.ng
Tags: