Sama da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ke hannunmu, Rundunar sojin Najeriya

Sama da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ke hannunmu, Rundunar sojin Najeriya

Fiye da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ne suka zub da makamansu ga sojojin yankin Arewa maso Gabas kamar yadda sojojin suka bayyana.

Kwamandan rundunar operation Hadin Kai, Manjo Janar Chris Musa, ya bayyana wa Channels TV yayin tattaunawar da suka yi da shi a ranar Litinin.

Sama da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ke hannunmu, Rundunar sojin Najeriya
Sama da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ke hannunmu, Rundunar sojin Najeriya. Hoto daga premiumtimes.ng
Asali: UGC

Ya bayyana yadda mazauna yankin suka dinga taimakon sojoji, musamman yadda suka samu bayanan sirri duk da cewa akwai bangaren da aka sanya wa shamakin sadarwa.

"Muna samun bayanai da zarar abubuwa sun faru", a cewar kwamandan.
"Wani lokacin, kalubalen da muke fuskanta shi ne hanyar sadarwa kasancewar ba ko ina bane ake samun kafar sadarwar ba; amma da zarar sun isa inda za su iya tuntubar mu suna tura mana sako.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

"Hakan ya taimaka mana kwarai wurin yakar 'yan ta'addan kuma mun samu natsuwar zuci sosai. Akwai 'yan ta'adda fiye da 51,000 da 'yan uwansu da suka yi mana mubaya'a."

Babu abin tsoro

Yayin da mutane da dama su ke ganin zubar da makaman 'yan ta'addan a matsayin nasarar yaki, wasu kuma a razane suke.

Janar Musa, a bangarensa, ya yarda da 'yan Najeriya, musamman mutanen da ke zama a yankin Arewa maso Gabas ba su da wata fargaba a ganinsa, saboda sojoji a tsaye suke kuma idansu a sanye ya ke akan 'yan ta'addan.

Ya ce sojoji sun dade suna kawo zaman lafiya a wasu kasashen, inda ya ce za su bi irin wannan salon wurin gyara a Najeriya.

Kwamandan OPH din ya ce ba komai bane don an yi fargaba amma tabbas su kwararru ne kuma ba wannan bane karonsu na farko na yin yaki ba.

Ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

"Idan sun yanke shawarar zub da makamai suna hanzarin zuwa wurin rundunar soji mafi kusa da su ne. Daga nan su bayar da makamansu.
"Akwai motocin da gwamnatin jihar ta tanadar wacce ta ke kwashe su zuwa sansanonisu inda dama an tabbatar da tsaronsu don a killacesu ta yadda ba za su zama kalubale ga kowa ba."

Borno: Sojin Najeriya sun bindige 'yan ISWAP 22, sun kwato makamai a tafkin Chadi

A wani labari na daban, dakarun jami'an tsaron hadin guiwa na kasashe (MNJTF) sun sheke 'yan Boko Haram 22 ko 'yan ta'addan ISWAP yayin da suke cin karensu ba babbaka a tafkin Chadi.

Babban kakakin rundunar MNJTF a N'Djamena na Chadi, Kamarudeen Adegoke ne ya tabbatar da hakan a wata takarda da ta fita ranar Lahadi, Premium Times ta ruwaito.

Adegoke, laftanal kanal, ya ce an sheke 'yan ta'adda a Tumbun Rabo cikin karamar hukumar Abadam a ranar 27 ga watan Afirilu.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 6 Yayin Da Suka Kai Wa Tawagar Kwamanda Hari a Taraba

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng