Gagararren mai garkuwa da mutane, Igbira, ya shiga hannun jami'an tsaro a Nasarawa
- 'Yan sandan jihar Nasarawa sun tabbatar da cafke fitaccen mai garkuwa da mutane, Mohammed Igbira
- Sun sanar da cewa, mutumin mai shekaru 45 a duniya ya dauka tsawon lokaci yana addabar jama'ar Akwanga da Wamba
- An gano cewa, Igbira ya ballo daga gidan yarin garin Jos ne da ke jihar Filato inda ya shigo gari ya cigaba da barna
Nasarawa - Rundunar 'yan sanda jihar Nasarawa ta bayyana yadda tayi ram da wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, mai shekaru 45, Muhammad Igbira, wanda ya dau tsawon lokaci yana hana mazauna karamar hukumar Akwanga da Wamba dake jihar kwanciyar hankali.
Punch ta tattaro yadda aka jefa shi wanda ake zargin da zama dan kungiyar masu garkuwa, gami da fashi da makami, gidan yari a Jos, jihar Fulatu, saboda hatsabibancinsa, amma daga bisani ya tsero zuwa jihar Nasarawa, inda yake cin karensa ba babbaka har zuwa lokacin da dubunsa ta cika.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel ne ya bayyana haka yayin zantawa da Punch a Lafia ranar Lahadi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Yayin da rundunar ta samu labarin cewa an ga kasurgumin hatsabibin a cikin garin Wamba, jami'an 'yan sandan Wamba suka hanzarta kai samame, inda suka yi ram da wanda ake zargin, Muhammad Ihbira mai shekaru 45.
"Bayan cigaba da bincike, an gano yadda wanda ake zarginsa da garkuwa da mutane, bayan yanke masa hukunci tare da jefasa gidan yarin Jos ya balle gidan yarin a 30 ga watan Nuwamba, 2021.
"A halin yanzu, 'yan sandan Najeriya da hukumar gidan yarin Jos, Fulato, sun gano wanda ake zargin, sannan rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta mika shi don cigaba da bincike."
Mai magana da yawun 'yan sandan ya kara da cewa, kwamishinan 'yan sandan, CP Adesina Soyemi, ya tura jami'an tsaron rundunar, dajika da biranen fadin kananan hukumomin jihar don tabbatar da an tsare rayukan mazauna yankin.
Kaduna: 'Yan sanda sun yi ram da 'yan ta'adda 2 dauke da miyagun makamai
A wani labari na daban, rundunar 'yan sanda jihar Kaduna ta bayyana yadda tayi ram da wasu mutum biyu da ake zargin 'yan ta'adda ne a cikin jihar, TVC News ta ruwaito.
Kakakin rundunar, Muhammad Jalige, a wata takarda da ya fitar ranar Laraba ya bayyana yadda aka kama wadanda ake zargi da bindiga kirar AK-47 guda biyu, carbin harsasai masu rai guda 32.
Ya kara da cewa, jami'an tsaron da suka yi amfani da dabarbarun sirri sun damko daya daga cikin wadanda ake zargin , mai shekaru 25 cikin karamar hukumar Giwa dake jihar.
Asali: Legit.ng