Jerin jihohi 23 da karin farashin wutan lantarki zai shafa
Gwamnatin tarayya ta sake bada izini ga kamfanonin rarraba wutan lantarki a Najeriya watau DISCOS izinin kara farashin wutar lantarki daga yanzu.
Hukumar lura da wutar lantarkin Najeriya NERC ce ta bayyana hakan a jawabin da ta saki.
Kamfanonin rarraba wutan da aka baiwa wannan izini sune Port Harcourt Electricity Distribution Company (PHEDC); Jos Electricity Distribution Company (JEDC); Kano Electricity Distribution Company (KEDC); Kaduna Electricity Distribution Company (KEDC); Ikeja Electricity Distribution Company (IKEDC) and Ibadan Electricity Distribution Company (IBEDC).
Wannan karon, jihohi 23 wannan kari zai shafa.
Dubi ga kamfanonin da aka baiwa izinin yin wannan kari, Legit ta tattaro muku jerin jihohin.
Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP
Ga jerinsu:
Kamfanin rarraba wutan Ikeja IKEDC
- Jihar Legas: Unguwannin Abule Egba, Akowonjo, Ikeja, Ikorodu, Oshodi, Shomolu
Kamfanin rarraba wutan Ibadan IBEDC
- Oyo
- Ogun
- Osun
- Kwara
- Wasu sassan jihar Neja
- Ekiti
- Kogi
Kamfanin rarraba wutan Jos JEDC
- Bauchi
- Benue
- Gombe
- Plateau
Kamfanin rarraba wutan Kaduna KEDCO
- Kaduna,
- Kebbi,
- Sokoto,
- Zamfara
Kamfanin rarraba wutan Kano KEDC
- Kano,
- Katsina,
- Jigawa
Kamfanin rarraba wutan PortHarcourt PHEDC
- Rivers,
- Bayelsa,
- Cross River
- Akwa-Ibom
Menene ya sabbaba yin wannan kari
NERC ta ce sun amince ayi wannan kari ne bisa wasu dalilai da abubuwan da suka yi la'akari da su.
Abubuwan sun hada da hauhawar farashin iskar Gas, hauhawar tattalin arziki, tashin farashin Dala, da kuma adadin lantarkin da ake da shi.
Yadda karin zai kasance
Kwastamomin A-Non MD dake biyan N56.16/kWh yanzu zasu fara biyan N60.67/kWh (Febrairu zuwa Disamba).
Kwastamonin B Non-MD dake biyan N56.64/kWh kuwa zasu fara biya N59.64/kWh
Kwastamonin E-MD2 kuwa dake biyan N50.72/kWh zasu fara biyan N54.22/kWh daga yanzu.
Asali: Legit.ng