Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada izinin kara farashin wutan lantarki

Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada izinin kara farashin wutan lantarki

  • Kuma dai, gwamnatin tarayya na shirin kara farashin wutan lantarki a kimanin jihohi ashirin da uku
  • Wannan ya biyo bayan lalacewa wutan lantarkin da aka yi fama tsohon watanni biyu a fadin tarayya
  • Jihohin da wannan kari zai shafa sun hada da Kano, Kaduna, Katsina, Legas dss

Birnin tarayya Abuja - Hukumar lura da wutar lantarkin Najeriya NERC ta baiwa kamfanonin rarraba wutan lantarki DisCos izinin kara farashin wutar lantarki.

Wannan ya bayyana a jawabin da Shugaban hukumar NERC, Sanusi Garba, da mataimakinsa, Musuliu Oseni, suka rattafa hannu mai ranar wata 29 ga Disamba, 2021.

A cewar rahoton TheNation, karin ya fara aiki ne daga watan Febrairun 2022.

Kamfanonin rarraba wutan da aka baiwa wannan izini sune Port Harcourt Electricity Distribution Company (PHEDC); Jos Electricity Distribution Company (JEDC); Kano Electricity Distribution Company (KEDC); Kaduna Electricity Distribution Company (KEDC); Ikeja Electricity Distribution Company (IKEDC) and Ibadan Electricity Distribution Company (IBEDC).

Kara karanta wannan

Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Buhari
Da duminsa: Gwamnati tarayya ta bada izinin kara farashin wutan lantarki
Asali: Facebook

NERC ta ce abubuwan da aka yi la'akari da su wajen kara farashin sun hada da hauhawar farashin iskar Gas, hauhawar tattalin arziki, tashin farashin Dala, da kuma adadin lantarkin da ake da shi.

Jawabin ya kara da cewa za'a cigaba da kara farashin bayan kowani wata shida.

Ya kara da cewa kwastamomin A-Non MD dake biyan N56.16/kWh yanzu zasu fara biyan N60.67/kWh (Febrairu zuwa Disamba).

Kwastamonin B Non-MD dake biyan N56.64/kWh kuwa zasu fara biya N59.64/kWh

Kwastamonin E-MD2 kuwa dake biyan N50.72/kWh zasu fara biyan N54.22/kWh daga yanzu.

Bidiyon matashi na tura wa 'yan NEPA karnuka yayin da suka zo yanke wuta

Wani faifan bidiyo na bidiyo ya nuna wani matashi da karnuka biyu yayin da ya tsare su daga tsorata jami'an NEPA.

Kara karanta wannan

Sunayen Soji 6 da yan bindiga suka kashe a harin kwantan bauna a Taraba

Kafar Instagram ta @Instablog9ja da ta sake yada faifan bidiyon ta ce matashin ya yi amfani da karnuka wajen hana wasu jami’an NEPA gudanar da aikinsu.

A cikin faifan bidiyon, an ga karnukan sun yi kamar sun shirya tsaf don farmakan jami'an. Bayan mutumin kuwa, an ga wani tsani jingine a jikin pole din wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng