Kudin wutan da ‘Yan Najeriya ke biya zai karu, Gwamnati ta yi na’am da karin farashi

Kudin wutan da ‘Yan Najeriya ke biya zai karu, Gwamnati ta yi na’am da karin farashi

  • Hukumar da ke kula da harkar wuta a Najeriya ta ba kamfanonin DisCos dama su kara farashinsu
  • Karin kudin zai fara aiki ne tun daga watan Fubrairun 2022 har zuwa karshen wannan shekarar
  • NERC ta ce sauyin farashin da aka samu zai shafi kamfanonin JEDC, KEDCO, IKEDC, PHEDC da IBEDC

Abuja - Hukumar NERC mai kula da harkar wuta a Najeriya ta yarda wasu kamfanonin da ke da alhakin raba wuta da kara farashinsu a shekarar nan.

Rahoton da The Nation ta fitar a ranar Alhamis ya bayyana cewa a Junairun 2022 aka amince da karin farashin amma daga watan Fubrairu zai soma aiki.

Kamfanonin da aka yarda su kara kudin su ne: Port Harcourt Electricity Distribution Company (PHEDC); da Jos Electricity Distribution Company (JEDC).

Sai Kano Electricity Distribution Company (KEDC); Kaduna Electricity Distribution Company (KEDCO); da Ikeja Electricity Distribution Company (IKEDC).

Kara karanta wannan

EFCC: Jonathan ya kawo shawarar karkatar da N2bn domin neman tazarce – Tsohon Gwamna

Na karshe shi ne kamfanin Ibadan Electricity Distribution Company wanda aka fi sani da IBEDC.

Tsarin MYTO 2022

Sanarwar ta fito ne a wata takarda da ta fito daga hannun NERC wanda aka yi wa take da “This regulatory instrument shall be cited as Multi-Year Tariff Order (MYTO-2022) for Port Harcourt Electricity Distribution Company Plc (PHED”).

Wutan lantarki
Na'urorin bada wutar lantaki Hoto: africa-energy-portal.org
Asali: UGC

NERC ta kafa hujja da tashin farashin kaya, tsadar gas, da karyewar darajar Naira da karfin samar da lantarkin a matsayin dalilin da ya sa aka kawo karin.

Hukumar ta ce an yi la’akari da wasu alkaluma kafin a dauki wannan mataki. Dama a tsarin MYTO, duk bayan watanni shida za a rika duba farashin.

Jaridar The Cable ta ce shugaban NERC da mataimakinsa; Sanusi Garba da Musiliu Oseni sun sa hannu a tsarin na MYTO da aka kawo tun Disamban 2021.

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Jefi Ma'aikatan Lantarki Da Duwatsu, Ta Kuma Lalata Musu Lada Yayin Da Suka Zo Yanke Mata Wuta

Yadda karin zai kasance

Karin da aka samu yana nufin wadanda ke rukunin PHED (A-Non MD) da suke biyan N56.16/kwh a farkon shekarar 2022, za su koma biyan N60.67/kwh.

Haka zalika ‘yan rukunin PHED (B Non-MD) za su dawo biyan N59.64/kwh daga N56.64/kwh.

Rahoton ya ce wadanda ke kan layin E- MD2 za su daina biyan N50.72/kwh, za su koma biyan N54.22/kwh daga Fubrairu zuwa karshen shekarar bana.

Kudin waya zai karu

A makon nan rahoto ya zo mana cewa watakila mutane za su ga canji wajen kudin da ake kashewa yayin yin waya ko aika sakonni ta salula a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta amince a kara haraji a kan wasu kayan waya. Jami’an kwastam za su rika karbar 5% a matsayin kudin shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng