Na kadu: Buhari ya yi Allah-wadai da fille kan ma'auratan sojoji biyu, ya dauki mataki

Na kadu: Buhari ya yi Allah-wadai da fille kan ma'auratan sojoji biyu, ya dauki mataki

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun ‘yan Najeriya domin jajantawa iyalan ma’auratan da ‘yan kungiyar IPOB da ESN suka kashe
  • An kai wa ma'auratan sojojin hari ne tare da kashe su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gudanar da bikin aure na gargajiya a jihar Imo
  • A halin da ake ciki, shugaba Buhari ya bayar da umarnin farauto wadanda suka aikata wannan ta'asar tare da gurfanar da su a gaban kuliya

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin soji da sauran jami’an tsaro da su yi iyakacin kokarinsu wajen kamo wadanda suka fille kan wasu sojoji biyu ma'aurata tare da gurfanar da su gaban kotu.

Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya yi Allah wadai da fille kan jami'an da kungiyar ‘yan ta’adda ta IPOB, ta yi a ranar Asabar, kamar yadda rundunar sojin Najeriya ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Buhari ya yi Allah wadai da kashe sojoji
Ban ji dadi ba: Buhari ya yi Allah-wadai da fille kan ma'auratan sojoji biyu, ya dauki mataki | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana yadda wasu sojoji biyu, Audu Linus da Gloria Matthew, suka mutu sakamakon fille kawunansu da aka yi a lokacin da suke kan hanyar zuwa jihar Imo domin bikin aurensu na gargajiya.

Shugaba Buhari ya jajantawa sojojin Najeriya da iyalan mamatan bayan da kungiyar ta'addancin ta harbe su, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari, wanda ya bi sahun ‘yan kasar nan wajen nuna matukar kaduwarsa tare da yin Allah wadai da ta’asar da 'yan ta’addan suka yi ya ce sam hakan rashin wayewa ne, kuma lamarin bai yi dadi ba.

Shugaban ya yi kira ga dukkan shugabannin al'umma, yanki da na kasa da su yi magana da murya daya, don nuna cewa kasar gaba daya tana adawa da wannan mummunan aiki na ta'addanci. Wannan ba abin yarda ba ne.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Ya ce:

"Tunaninmu da addu'o'inmu suna tare da iyalan wadanda wannan lamari mai ban tausayi da ban haushi ya faru dasu."

Abinda Yasa Muka Fille Wa Soja Da Matarsa Kai a Hanyarsu Na Zuwa Ɗaurin Aurensu, Ɗaya Cikin Makasan Ya Magantu

A tun farko, kisan gillar da aka yi wa wani soja, A. M Linus da matar da ya ke shirin aure, yayin da su ke hanyarsu da zuwa Jihar Imo ya janyo cece-kuce a kasar nan.

Bayan kisan ne wani dan bindiga wanda ya ce yana cikin wadanda su ka yi ajalinsu ya bayyana dalilinsu na tafka laifin.

An samu rahoto akan yadda su ke hanyarsu ta zuwa bikin aurensu kafin ‘yan ta’addan su tare su su kuma datse musu rayuwarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.