Sallah: Masarauta ta dakatar Hakimai, ‘Dan Majalisa bayan hawan idi saboda saba doka

Sallah: Masarauta ta dakatar Hakimai, ‘Dan Majalisa bayan hawan idi saboda saba doka

  • Masarautar Zazzau a karkashin jagorancin Sarki Ahmed Nuhu Bamalli ta dakatar da wasu Hakimai
  • Wadannan Hakimai da wasu masu sarauta sun yi amfani da ‘yan daba ne a wajen hawan sallar idi
  • Hadimin masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai ne ya bada wannan sanarwa bayan an yi bikin sallar

Kaduna - Mai martaba Sarkin Zazzau, Amb. Ahmed Nuhu Bamalli ya dakatar da wasu Hadimai hudu jim kadan bayan an sauko daga karamar sallah.

Daily Trust ta ce wannan sanarwa ta fito ne daga bakin mai magana da yawun masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna, Abdullahi Aliyu Kwarbai.

A ranar Litinin, 2 ga watan Mayu 2022, Alhaji Kwarbai ya ce dakatarwar da aka yi wa wadannan sarakai za ta fara aiki ba tare da wani bata lokaci ba.

Jawabin Abdullahi Aliyu Kwarbai ya ce wadanda aka dakatar sun hada da Alhaji Bashir Shehu Idris, Uban garin Zazzau wanda shi ne Hakimin Soba.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

Jami’in yada labarai da hulda da manema labarai na masarautar ya ce an dakatar da Sarkin Dajin Zazzau, Hakimin Kubau, Alhaji Shehu Umar Aliyu.

Jaridar ta ce sauran wadanda aka dakatar sun hada da Wakilin Birnin Zazzau, Hon. Suleiman Ibrahim Dabo wanda ‘dan majalisa ne mai wakiltar Zaria.

Sarkin Zazzau
Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli Hoto: @masoyin.sarkiahmadu
Asali: Facebook

Haka zalika an kuma dakatar da Garkuwan kudun Zazzau watau Alhaji Muhammad Sani Uwais. Garkuwan kudun shi ne jami’in kula da kudi a FCE Zaria.

Meyasa aka dauki wannan mataki

Sanarwar ta ce wadanda aka dakatar sun saba dokar masarauta ta hawan sallah domin sun yi amfani da ‘yan tauri da su ka rika fito da makamai a tawagarsu.

“Dokar ta haramtawa masu rike da sarauta amfani da ‘yan daban da ake kira ‘yan yauri, wadanda su ke nuna makamai a lokacin da ake hawa.”

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi ya yi maza ya yi karin-haske, ya karyata jita-jitar goyon bayan Osinbajo

“Kuma Hakimai hudu sun taka wannan doka a wajen bikin hawan sallar idi da aka yi, duk da jerin gargadin da aka rika yi.” – Abdullahi Kwarbai.

Bayan zaman Ahmed Nuhu Bamalli Sarkin Zazzau a 2020 yake ta kawo wasu gyare-gyare a fada.

Kadi ya zama Wazirin Zazzau

A karshen shekarar bara ne ku ka samu rahoto cewa Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya zabi Alkali Muhammad Inuwa Aminu a matsayin Wazirinsa.

Mai martaba Sarkin Zazzau ta bakin Barau Musa Aliyu ya ce Alkali Muhammad Inuwa Aminu ne zai maye gurbin Wazirin da aka Mai martaba ya tunbuke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng