Za ayi babban nadi a Zazzau, Mai martaba Ahmad Bamalli ya zabi sabon Waziri bayan tsige Aminu

Za ayi babban nadi a Zazzau, Mai martaba Ahmad Bamalli ya zabi sabon Waziri bayan tsige Aminu

  • Za a nada Alkali Muhammad Inuwa Aminu a matsayin sabon Wazirin Zazzau
  • Sarkin Fulani, Alhaji Barau Musa Aliyu ne ya sanar da wannan a wata wasika
  • Masarautar Zazzau za ta maye gurbin Wazirin da Gwamnati ta dakatar a 2020

Kaduna – Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya zabi Alkali Muhammad Inuwa Aminu a matsayin sabon Waziri.

A wata takarda da ta fito daga masarautar Zazzau, Mai martaban ya sanar Khadi Muhammad Inuwa Aminu cewa zai ba shi sarautar Wazirin kasar.

Wasikar da aka aika wa Muhammad Inuwa Aminu ta shiga hannun Legit.ng Hausa, inda aka tabbatar masa da sarautar a ranar 11 ga watan Oktoba, 2021.

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da wannan zabi da Sarki Ahmad Nuhu Bamalli ya yi. Abin da ya rage shi ne sa ranar da za a nada wa Aminu rawani.

Kara karanta wannan

Allah ya yi wa matar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi rasuwa

A takardar, an yi kira ga sabon Wazirin na Zazzau ya zama mai fadan gaskiya da rike amana. A watan Nuwamban nan Bamalli ya cika shekara a sarauta.

Wasikar Ahmad Bamalli
Nadin sabon Wazirin Zazzau Hoto: Legit Hausa
Asali: Original

Abin da takardar ta kunsa

“Bayan gaisuwa mai yawa.”
An umarce ni in sanar da kai cewa, bisa umarnin gwamnatin jihar Kaduna ta ranar 20/9/2021, a takardarta mai lamba GH/KD/S78, Mai martaba Sarkin Zazzau, ya tabbatar maka da sarautar Wazirin Zazzau, kuma babban ‘dan majalisar Sarki a yau Litinin, 11/10/21.”
“Mai marataba Sarkin Zazzau da al’ummar masarautar Zazzau suna taya ka murna da fatan alheri.”
“Kuma da fatan za ka rike amanar masarautar Zazzau da kawo cigaba da fadin gaskiya a kowane hali da kuma yin aiki da dokokin Allah (SWT).
“Muna taya ka murna” - Sarkin Fulanin Zazzau, Sakataren fada.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Jerin Jiga-jigan APC 10 da suka kai karar Gwamna Ganduje wajen uwar Jam’iyya

Legit.ng ta fahimci cewa wannan takardar ta fito ne daga sakataren masarautar Zazzau, Barau Musa Aliyu wanda yake rike da sarautar Sarkin Fulani.

Dakatar da Ibrahim Aminu, a 2020

A Nuwamban shekarar 2020 ne aka ji cewa gwamnatin Jihar Kaduna ta dakatar da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, daga kan mukamin da yake kai.

Masana tarihin sarautar gargajiya sun ce Wazirin Zazzau na cikin manya a majalisar Sarki, sannan shi ne babba a majalisar masu zaben Sarki a kasar Zazzau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel