Wankan Sallah: Hotunan Buhari, mukarrabansa da danginsa a ranar karamar sallah
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci filin idin barikin Mambila a babban birnin tarayya Abuja
- Shugaban dai ya bi sahun sauran musulmin Najeriya ne wajen gudanar idin karamar sallah ta shekarar 2022
- Hotuna sun nuna shugaban tare da danginsa, iyalansa da wasu mukarrabansa jim kadan bayan idar da sallar
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun sauran musulmi a Najeriya, ya harkaci sallar idi a babban birnin tarayya Abuja.
Wata sanarwar da hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau ya fitar ta shafin Facebook ta nuna hotunan shugaban lokacin da ya halarci sallar a barikin Mabila da ke Abuja a yau Litinin, 2 ga watan Mayu.
Hotunan sun nuna shugaban cikin farin ciki, yana daga wa jama'a hannu.
'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya
Wani yankin sanarwar ya ce:
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci Sallar Eid Al-Fitr a barikin Mambila, Abuja ranar 2 ga Mayu, 2022."
Hakazalika, sanarwar ta kuma nuno shugaban tare da danginsa; a fadar shugaban kasa bayan dawowarsu daga sallar idin da aka gudanar yau.
Sanarwar ta ce:
"Shugaba Buhari tare da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da wasu 'ya'yansu, jikoki, da 'yan uwansu bayan halartar Sallar Idin Sallah a barikin Mambila, Abuja ranar 2 ga Mayu, 2022."
Baya ga ganawa da daniginsa bayan sallar, shugaban ya kuma gaisa da wasu mukarabbansa da jiga-jigan gwamnatin Najeriya.
A cewar Buhari Sallau:
"Shugaba Buhari tare da wasu mukarrabansa bayan halartar Sallar Eid Al-Fitr a barikin Mambila, Abuja ranar 2 ga Mayu, 2022."
Kalli hotunan a kasa:
Shirin 2023: Yahaya Bello ya gana da Buhari domin nuna masa fom din takarar shugaban kasa
A wani labarin na daban kun ji cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari karbi bakuncin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello a fadarsa da ke Aso Rock Villa da ke Abuja.
Ganawar tasu ta zo ne daidai lokacin da gwamnan ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki gabanin zaben fidda gwani.
Fadar shugaban kasa ta ce, gwamnan ya gana da Buhari a yau Alhamis 28 ga watan Afrilu, kamar yadda hadimin shugaba Buhari ya yada wasu hotunan shugaban da gwamnan ta shafin Twitter.
Asali: Legit.ng