Abubuwa 25 da ya kamata duk Musulmai su sani a game da bikin idi a shari’ar musulunci

Abubuwa 25 da ya kamata duk Musulmai su sani a game da bikin idi a shari’ar musulunci

  • A ranar Litinin 2 ga watan Mayun 2022 ne Musulmai su ke yin bikin sallar idi a kasashe da-dama
  • Najeriya ta na cikin kasashen da za ayi sallah a yau a sakamakon rashin ganin watan a ranar Asabar
  • Addinin musuluncin ya yi wasu tanadi na musamman a game da wannan biki na karamar sallah

A wannan rahoto na goron sallah, mun tsakuro wani bayani ne da Shehin malami, Dr. Kabir Asgar ya yi a shafinsa na Facebook a game da bikin idi.

Da farko malamin ya ce Idi shine bikin da sharia ta tanadar wa musulmai a madadin bukukuwan maguzanci ko al’adun da sharia ba ta yarda da su ba.

Dr. Asgar wanda malamin harshen larabci ne a jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke garin Zaria ya jero wasu abubuwa da ake bukata ga musulmai a yau.

Kara karanta wannan

Batanci Ga Annabin Rahma (SAW), Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Malamin ya ce ana so mata da maza duk su fita zuwa wajen sallah a cikin kaya masu kyau.

Ba a yin nafila a wurin sallar idi, amma akwai kabarbari da ake yi. Manzon Allah SAW ya kan yi limanci da surori irinsu Qaf, Qamar, A'ala ko Ghashiyah.

Abubuwa 25 da za a kiyaye

1. Sallar Idi sunna ce mai ƙarfi; Ba shi kyautuwa mutum ya bar ta ba tare da larurar da ta sha gabansa ba.

2. Sunna ta nuna a fita bayan gari ne a yi sallar idi in dai ba akwai larura ba.

3. Ana so kowa ya fita zuwa sallar idi da suturasa mafi kyau (sababbi ko wankakku).

4. Ana so mata da yara da tsofaffi su fita. Har da mata masu haila. (Amma ba za su yi sallar ba).

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

5. Wadanda basu da suturar fita anguwa babu laifi su ara a wajen ƙawaye ko ‘yan uwa ko abokan zamansu.

6. Ana yin sallar idi ne da hantsi, an so a jinkirta sallar azumi kamar yadda kuma aka so a yi ta layya da wuri.

7. An fi son mutum ya je filin idi da ƙafa matuƙar ba wata wahala ko nisa. Sannan ana son canza hanya in za a dawo.

8. Liman zai yi wa mutane sallah raka’a biyu da huɗuba a bayan sallar.

9. Manzon Allah (SAW) ya kasance yana karanta (سورة ق) da (اقتربت الساعة) a sallolinsa na idi. Wani lokacin kuma ya karanta (سورة الأعلى) da (سورة الغاشية)

10. Zahirin hadisai ya nuna cewa Manzon Allah (SAW) yana yin huɗuba ne guda ɗaya. Sai dai malaman da dam suna ganin cewa za a yi huɗubar ne kamar yadda ake yin huɗubar Sallar Juma'a.

Musulmai a idi
Musulmai su na sallar idi Hoto: www.nytimes.com
Asali: UGC

11. Liman ba ya yin nafila kafin ko bayan sallar idi. Amma an samo daga magabata cewa sukan yi nafila kafin sallar idi da bayan ta a filin idin ko a hanya ko a masallatan cikin gari.

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi ya yi maza ya yi karin-haske, ya karyata jita-jitar goyon bayan Osinbajo

12. Ana son mutane su yawaita kabarbari tun daga wayewar garin sallah har yammacin karshen kwanakin tashreeƙ. Ƙaramar Sallah ba ta da kwanakin Tashreeƙ

13. An so a tafi filin idi a kafa kuma a canza hanya a yayin dawowa gida

14. An so wanda zai yi layya ya kame baki daga cin wani abu har sai an yanka dabbarsa sannan ya ci daga sashen namanta

15. A sallah ƙarama kuwa ana son mutum ya ɗan ci wani abu kafin tafiya filin idin.

16. Akwai kashedi da Annabi (SAW) ya yi ga wanda ke da halin layya amma ya ƙi yi. (cewa kar ya kusanci filin idin musulmi)

17. Idan idi ya haɗu da Juma’a, wanda ya halarci idi to wajabcin juma’a ya faɗi a kansa. Amma halartar duka idi biyun (idi da juma’a) ya fi falala.

18. Wanda kuma ya ɗauki sassaucin bai yi laifi ba. Amma zai yi azahar a gida ko a masallacin anguwarsu shi kadai ko tare da ire-irensa.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

19. Wanda bai sami idi ba zai rama, sannan zai je juma’a a bisa wajabci.

20. Babu laifi yi wa juna barka da sallah bisa abin da yake sananne a sharia da al'ada mai kyau.

21. Babu laifi gudanar da sauran harkokin bikin sallar da al’adun da ba su saɓa wa shariar musulunci ba.

22. A guje wa ganganci da ababen hawa da sunan murna.

23. A guje wa fitar mata da yara barkatai.

24. A guje wa sanya suturun da suka saɓa wa sharia da al’ada ta gari.

25. Kamar yadda aka yi bayani tun farko, Idi shine bikin da sharia ta tanadar wa musulmai.

Kura-kuren Ramadan

A wani wa’azi da ya yi a shafinsa na Facebook kwanakin baya, kun ji cewa Dr. Kabir Asgar ya yi kokarin fito da kura-kuren da ake yi a wajen yin sallar dare.

Malamin addinin ya yi wannan fadakarwa ne ganin an shigo kwanakin goma na karshe a watan nan mai alfarma na Ramadan domin ya ja hankalin jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel