Jerin wasu manya da kananan kura-kurai da Musulmai suke yi a wajen sallar dare

Jerin wasu manya da kananan kura-kurai da Musulmai suke yi a wajen sallar dare

  • Dr. Kabir Asgar wanda aka fi sani da Asgar ya fadakar da al’ummar musulmai a game da tahajjud
  • Shehin Malamin ya jero wasu kura-kurai da Musulmai su kan yi a yayin da ake yin sallar tsakar dare
  • Asgar malamin harshen larabci ne a jami’ar ABU Zaria, kuma dalibin Marigayi Sheikh Albani Zaria

Kaduna - A wani wa’azi mai fadakarwa da ya yi a shafinsa na Facebook, Dr. Kabir Asgar ya yi kokarin fito da kura-kuren da ake yi a wajen sallar dare.

Malamin addinin ya yi wannan fadakarwa ne ganin an shigo kwanakin goma na karshe a watan nan mai alfarma na Ramadan da ake son yawan ibada.

Na farko a jerin da Asgar ya kawo shi ne cakuduwar maza da mata a wajen sallar tsakar daren.

Kara karanta wannan

Kyakkyawan karshe: Yadda Mutuwa ta Dauki Matashin Limami a Tsakiyar Sallar Dare

Kure-kuren sun hada da wasu bidi’o’i da aka shigo da su, da sakaci wajen karanta Kur’ani tiryan-tiryan kamar yadda Annabi Muhammad SAW ya koyar.

Malamin da yake karantarwa a jami’ar ABU Zaria da makarantar Darul Hadith Salafeeyah ya ce yana cikin kuskure tunanin cewa bai halatta mata su fita sallah ba.

Daga cikin abubuwan da aka yi fice da Asgar ya ce akwai kuskure a yinsu akwai yin addu’ar nan ta saukar Kur’ani da tsawaita addu’ar wutiri da wasu ke yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A addinin musulunci, malamin ya ce babu dalilin a ce dole sai an yanka albashi ga limaman tahajjud ko a rika kokarin sallar yayin da ake jin mugun barci.

Masu sallar dare
Sallar Tahajjud a kasar Turkiyya Hoto: www.dailysabah.com
Asali: UGC

Ga jerin nan kamar haka:

1. Cakudedeniyar maza da mata

2. Daga ido sama a lokacin addu'ar wutiri

3. Dagewa wajen yin sallar dare bayan barci ya galabaici mai yi

Kara karanta wannan

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

4. Ware wata rana guda ɗaya da ake tsammanin Lailatul Ƙadr ce da tsayuwa tare da watsi da sauran dararen

5. Dauke-dauken hotunan sallar dare (selfie da makamantansa) da yada su a social media

6. Fifita yin sallar dare (a watan Ramadan) a gida maimakon bin jam’i a masallaci

7. Fita daga masallaci kafin a gama sallar dare ko kafin a yi wutiri

8. Fitar mata zuwa wajen sallar dare ba tare da bin ƙa’idojin sharia wajen fitar ba

9. Gabatar da wa’azi na musamman a tsakanin raka’o’in sallar dare

10. Wofantar masallatai daga tarawih a goman ƙarshen Ramadan da kuma sake fitowa don yin tahajjudi

11. Karanta Al-Ƙur’ani da sauri (ba tare da tajweed ba) don a yi marmaza a sauka

12. Kasancewar karatun wani masallaci yana shiga cikin wani saboda ƙaran loudspeaker

13. Ƙin bin sallar dare da gangan har sai an gama karatu ko an kusa ruku’u

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

14. Ƙin yin sallar dare a masallacin anguwarku da tafiya wani masallaci na nesa

15. Kiran sallah ko fadin (الصلاة جامعة) don sanar da lokacin sallar dare

16. Ƙirƙirar zikirori kala dabam-dabam wadanda ake yi bayan kowace sallama

17. Ƙokarin yin kuka da ƙarfin tsiya don nuna tsoron Allah

18. Lazimtar yin saja’i a adduar wutiri

19. Maishe da sallar dare wajen neman taimako da tara sadaka

20. Ƙudurce cewa a daren LAILATUL ƘADRI ba a ganin komai sai Ka’abah!

21. Ƙudurce cewa bai halasta mata su je sallar dare ba

22. Ƙudurce cewa dole sai an sauke Al-ƙur’ani a cikin kwanakin sallar

23. Ƙudurce cewa sai masallaci ‘kaza’ ko bayan limami ‘wane’ kawai zan yi sallah

24. Ƙudurce cewa sallar dare bidi’a ce ƙyaƙƙyawa

25. Rage yawan fitillun masallaci da tunanin wai in akwai duhu an fi samun natsuwa

26. Rashin sanin fiqihun yi wa liman gyara a tilawa da gaggawar yi masa gyara kafin ya tabbata ya yi kuskure ko mantuwa

Kara karanta wannan

Zamfara: Bayan Raba Wa Sarakuna Cadillac, Matawalle Ya Tura Malamai 97 Umrah Don Yin Addu'a Kan 'Yan Bindiga

27. Rera addu’ar wuriti kamar yadda ake tilawar Al-ƙur’ani

28. Rike Al-ƙur’ani a lokacin sallah ga mutumin da ba limami ba kuma mai sallah shi kaɗai ba

29. Sakaci da sallolin farilla da bai wa nafila muhimmanci

30. Sanya sautin amsa kuwwa (loudspeaker) fiye da buƙata

31. Sanya wa limamin sallar dare albashi ko biyan sa kuɗin jan sallar dare

32. Tsawaita addu’ar wutiri fiye da misali

33. Watsi da sallar dare bayan Ramadan sai Allah ya kai mu baɗi!

34. Wuce iyakar da sharia ta gindaya a wajen adduo’i da bai wa buƙatun duniya muhimmanci fiye da na lahira

35. Yin adduar da aka fi sani da suna (دعاء ختم القرآن) watau (Adduar sauka)

36. Yin sallar dare a daren sallah (bayan an ga wata)

37. Yin sallar dare fiye da adadin raka’o’in da ya tabbata a sunna

38. Yin sallar wutiri ta yi kama da yanayin sallar magriba

Kara karanta wannan

Dakarun hadin gwiwa sun yi gagarumin nasara: Sun kashe kwamandojin ISWAP 10 da mayaka 100 a tafkin Chadi

39. Zaman fira (ana cikin sallah mutum ya yanke ya kafa fira da na kusa da shi ko buga waya)

40. Zuwa wajen sallar dare da darduma ko sallaya ta musamman

Liman ya rasu a wajen sallar dare

A lokacin da Musulmai ke azumin Ramadan, kuma aka shigo goman karshe, sai mu ka kawo maku labarin mutuwar wani Ustazu a wajen sallar dare.

Malam Sani Lawan ya rasu bayan ya yi sujuda ga Allah, ya na mai limancin sallar tahajjud a daren 23 ga watan Ramadan a garin Zaria a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng