Siyasa babu gaba: Yadda shan ruwan Ramadan ya hada shugabannin matasan APC na PDP

Siyasa babu gaba: Yadda shan ruwan Ramadan ya hada shugabannin matasan APC na PDP

  • Gidauniyar Ameer Foundation ta shiryawa matasa wani buda baki na musamman na watan azumi
  • Mohammed Kadande Sulaiman da Dayo Israel sun samu halartar wannan bikin shan ruwa da aka yi
  • Shugabannin matasan na jam’iyyun na PDP da APC sun yi kira ga matasa su guji shiga rikicin zabe

A ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu 2022, shugabannin matasa na manyan jam’iyyun Najeriya watau PDP da APC suka zauna a teburi daya.

Shugabannin matasan jam’iyyun sun hadu a wajen taron buda baki da gidauniyar Ameer Foundation ta shiryawa Musulmai da kiristoci.

Legit.ng Hausa ta fahimci gidauniyar da (Dr.) Ameer Lukman Haruna yake jagoranta ta shirya shan ruwan don hada-kan matasa mabiya addinai.

Taron yayi sanadiyyar haduwar Mohammed Kadande Sulaiman da kuma Dayo Israel da sauran jagororin matasa da ‘yan kishin kasa a garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Kamar yadda shugaban matasan APC na kasa, Dayo Israel ya shaida a shafinsa na Twitter, ya zauna da Kadade Sulaiman na jam’iyyar hamyya.

Prince Mohammed Kadande Sulaiman da Dayo Israel
Prince Mohammed Kadande Sulaiman da Dayo Israel @mohammed.kadade
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Dayo Israel

“A jiya ni da shugaban matasa na jam’iyyar APC da gungun matasa ‘Yan Najeriya daga jam’iyyun siyasa dabam-dabam mun yi buda-baki tare.”
“Mun samu damar saida jam’iyyunmu, kuma mun amince mu yi kira ga matasa su kauracewa shiga harkar rikicin zabe a zabe mai zuwa.”

Kiran da Kadade ya yi

Shi ma takwaransa na PDP ya tabbatar da wannan haduwa a shafinsa na Facebook, ya ce AMEER Foundation ta gayyace shi shan ruwa tare da su Dayo Israel.

“An samu damar tattaunawa a game da kalubalen da damammakin matasa domin mu ne ke dauke da fiye da 50% na masu yin zabe a Najeriya.”

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

“Mun yarda za mu tallata jam’iyyun siyasan, kuma mu karfafawa matasa shiga cikin harkar zabe.”

Har ila yau Kadade ya shaida cewa ya yi kira ga matasa su hada-kai da su domin ganin jam’iyyar PDP ta karbi jagorancin gwamnatin tarayya a zaben 2023.

Ameer Lukman Haruna ya ce taron zai hada kan mabiya addinai, ya kawo zaman lafiya a lokacin da marasa kishin kasa ke kokarin raba kan al'ummar kasar.

Legit.ng Hausa ta tuntubi wanda ya hada wannan taro, inda ya shaida mana cewa wasu za su biyo baya. Ya ce, In sha Allah, nan gaba za a kira wasu taron.

Ameer Haruna ya ce wannan ne karo na uku da aka yi irin wannan zama. An shirya buda-baki a garuruwan Kaduna, Jos, Kano da kuma birnin tarayya Abuja.

An kai jam'iyyar PDP kotu

A makon da ya gabata aka ji cewa Hon. Cosmas Ndukwe ya hakikance a kan cewa lokacin mutanen Kudu maso gabas ne su shugabanci Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanatan Kebbi ta tsakiya: Alaka ta yi tsami tsakanin Aliero da Gwamna Bagudu kan wanda zai mallaki tikitin APC

Babban jigon na PDP a jihar Abia ya kai karar jam’iyyarsa a kan wannan a wani kotu da ke Abuja. Ndukwe ya bukaci PDP ta warewa yankinsa tikiti a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng