Tsohon Daraktan Hukumar DSS, Bukar Shettima, ya riga mu gidan gaskiya

Tsohon Daraktan Hukumar DSS, Bukar Shettima, ya riga mu gidan gaskiya

  • Tsohon shugaban hukumar tsaro DSS reshen Kaduna, Alhaji Bukar Shetima, ya rasu bayan fama da doguwar rashin lafiya na tsawon shekaru
  • Bayanai sun nuna cewa Alhaji Bukar ya rasu ne yau Lahadi da safe, kuma za'a gudanar da Jana'izarsa da yamma a masallacin Sultan Bello
  • Mamacin ya rasu ya bar ƴaƴa da jikoki, daga cikin 'ya'yansa akwai shugabar Bankin Unity na shiryyar Kaduna, Hajiya Hamsatu Bukar Shetima

Kaduna - Tsohon Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a jahar Kaduna, Alhaji Bukar Shetima, ya riga mu gidan gaskiya.

Duk da cikakken bayani kan rasuwarsa ya yi wahala, amma jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Alhaji Shetima ya rasu ne ranar Lahadi da safe.

Tsohon daraktan DSS, Alhaji Bukar Shetima.
Tsohon Daraktan Hukumar DSS, Bukar Shettima, ya riga mu gidan gaskiya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa Marigayin ya rasa rayuwarsa ne bayan fama da doguwar rashin lafiya na tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Kazalika wasu bayanai sun nuna cewa za'a gudanar Jana'izar marigayin a babban Masallacin Sultan Bello dake Kaduna yau Lahadi da yamma.

Tsohon Daraktan ya rasu ya bar 'ya'ya waɗan da suka yi suna da kuma jikoki da dama.

Daga cikin 'ya'yan da marigayin ya mutu ya bari akwai shugaban kamfanonin Barbedos Group, Alhaji Kashim Bukar Shetima, da kuma shugaban Bankunan Unity dake shiryyar Kaduna, Hajiya Hamsatu Bukar Shetima.

Wasu sun yi Sallar Eid-El-Fitr a Sokoto

A wani labarin kuma Wasu Musulmai sun saba Umarnin Sarkin Musulmai, sun gudanar da Sallar idi a Sokoto

Wasu al'umma mabiya Addinin Musulunci a Sokoto sun gudanar da Sallar Eid-El-Fitr yau Lahadi inda suka saba wa umarnin Sarkin Musulmai.

Mutanen waɗan da mafi yawancin su mabiya Shekih Musa Lukwa ne, sun yi Sallah da misalim ƙarfe 8:00 na safe bayan tabbatar da ganin wata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262